Arsenal za ta iya ajiye fan miliyan 63 bayan an tunatar da Mikel Arteta cewa idan Yana son mallaki Serge Gnabry.
Serge Gnabry bai kamata ya Zama zabin farkon da Arsenal ke nema ba a lokacin bazara, ba musamman idan Nicolas Pepe ya ci gaba da zama a kungiyar. Arsenal
Serge Gnabry ya kasance akan gaba acikin labaran ‘yan wasa na kwanan nan saboda halin da ake ciki a kwantiraginsa da Bayern Munich, amma hakan bai kamata ya sanya Arsenal taji ta mallake shi ba
Duk da cewa dan kasar Jamus din ya samu kyakykyawan lokaci a duk tsawon rayuwarsa ta Bayern, tarihin shi dai kwallaye da ya zira a raga a kakar wasan da ta wuce Bai Kai Wanda Nicolas Pepe, ya zura ba wanda ya yi kokarin shiga tawagar Mikel Arteta.,
Arsenal dai na matukar bukatar dan wasan da ya taka rawar gani wajen zura kwallo a raga, kuma hakan ya kamata a maida hankali a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara.
Duk da yake Gnabry tabbas zai taimakawa Gunners, idan yazo Arteta ya riga ya sami Yan wasa masu ƙarfi a cikin wuraren da , dama
Gnabry ya zira kwallaye 11 a kakar wasa ta 2020/21, inda goma daga cikinsu sun zo a Bundesliga da sauran a cikin DFB-Pokal.
Pepe ya samu nasarar zura kwallaye 16 a kakar wasan da ta wuce, 10 ya zo a gasar, wanda yayi daidai da Gnabry, da kuma sauran kwallaye shida a gasar ta Europa. , kuma a bayyane yake cewa Gnabry zai iya ba Gunners ƙarin barazanar kai hari bayan ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da Bayern Munich ta samu a gasar zakarun Turai a 2020. Ko Bayyana mana Ra'ayin ku,