A cewar Marca, Martin Odegaard har yanzu yana muhawara inda zai taka kwallon kafa a kakar wasa mai zuwa bayan ya damu matuka game da matsayin sa a cikin tawagar Carlo Ancelotti.
Dan wasan na Norway ya ji yana da kyakkyawar dama ta Buga kwallon kafa ta yau da kullun a Bernabeu lokacin da ya koma Spain bayan watanni shida a matsayin aro a Arsenal amma tare da Casemiro, Luka Modric, Toni Kroos, Isco, da Federico Valverde a gaba. ya fara nuna damuwar shi wataƙila ba zai samu damar Buga Wasa Koda yaushe ba.
Wani Rahoton
ya yi iƙirarin cewa Odegaard yana son "jin cikakken magana idan zai buga ƙwallo a Real Madrid Koda yaushe
Kungiyar ta Real Madrid ta Kokarin tara kuÉ—i a wannan bazarar (saboda har yanzu suna da burin siyan Kylian Mbappe), Madrid ta bayyana É—an wasan tsakiyar mai shekaru 22 da Dani Ceballos a matsayin manyan 'yan Wasa biyu da za'a iya siyar daya za su siyar da zarar Raphael Varane ya kammala komawa Manchester United.
Ba wani sirri bane cewa Gunners sun shigo bazara tare da Odegaard akan jerin siyayya. Mikel Arteta ya gamsu da halayen É—an wasan yayin zaman sa a Emirates kuma ya yi hanzarin turawa zuwa ga aro.
James Maddison da Houseem Aouar su ne sauran jita -jitar da ake son cimmawa idan yarjejeniyar Odegaard ta gaza cimma ruwa.