Gabriel Magalhaes ya ce yana kulla alaka da William Saliba a ciki da wajen filin wasa kuma ya bayyana cewa suna tattaunawa da juna cikin Faransanci.
Fahimtar Gabriel a cikin harshe ya samo asali ne daga shekaru uku da yayi tare da Lille Hakan yasa yake iya Tattaunawa da harshen Saliba yayin da Ingilishi bai inganta.abakin shi ba
A wata hira da ya yi da Sky Sports gabanin karawar da za su yi da Leicester ranar Asabar, Gabriel ya ce: “Shi matashin dan wasa ne da ya zo nan tun yana karami, sannan ya fita don samun kwarewa.
“Yanzu, duk da shekarunsa, ya riga ya buga wa tawagar kasar Faransa wasa. Wannan ya gaya maka yadda yake da kyau. Ya zo nan don taimakawa ƙungiyarsa kuma yana da basira mai ban sha'awa.
“Shi abokina ne mai kyau. Muna magana da Faransanci tare, don haka yana taimakawa. Ya kara kwarewa sosai a kungiyar kuma ina ganin yana da kyakkyawar makoma a gabansa."
“Na yi shekara biyu a nan, don haka ina da gogewa da zan iya amfani da shi don taimaka masa,” in ji Gabriel.
“Amma a lokaci guda, zai iya taimaka mini. Yana da inganci mai yawa da ƙarfin jiki mai yawa a cikin filin wasa. Muna da halaye iri ɗaya. Ina ganin muna kyautata wa junanmu."
A halin yanzu, Gabriel ya bayyana gamsuwa da haduwarsu kuma ya yi watsi da maganar fitarsa zuwa wata kungiyar,
Dangane da alaka da wasu kungiyoyi a Turai, ya ce: "A koyaushe yana da kyau a sami wannan karramawa amma na mai da hankali sosai kan Arsenal.
“Na yi farin ciki sosai a nan. Ina da kyakkyawar alaƙa da abokan aikina kuma na himmatu sosai ga aikin. Ina da yakinin cewa, da aikin da muke da shi, za mu iya cimma abubuwa da dama."
Rabi'u Umar