BAN GAMSU DA WASAN ARSENAL BA!!

BAN GAMSU DA WASAN ARSENAL BA!!


Duk da kasancewar Arsenal ta doke Liecester City daci 4-2 to amma magana ta gaskiya ban gamsu da wasan da Arsenal ta buga ba.

Akwai bukatar Arteta yayi gyara sosae ga yan wasansa musamman Martin Odegard. Kwata kwata baya buga ball da kishi wasa kawai yake acikin fili domin kuwa ana saurin amsar kwallo a ƙafarsa.

Haryanzu Saka bai fara buga kwallo kamar yadda nasanshi ba, yana buga wasa kamar akwai gajiya ajikinsa.

Thomas Partey (Yakubu) yana kokari wurin tare sosae, to amma passing nashi suna yawan zama error.

Arsenal sun bawa Liecester dama sosae a wasan. Baikamata ace Liecester City sun iya sakawa Arsenal kwallaye har biyu a raga ba kwata kwata.

Ina son ganin team din Arsenal ta kasance wadda duk wadda ta kama sai jikinsa ya gaya masa a dinga kwallo kamar daga ranar bazasu sake buga wasa ba. A hana team ganin kwallo. 

To zuwa yanzu kwata kwata ban gamsu da wasan ba.

Amma yanzu aka fara ina fatan Arteta zaiyi gyara sosae.

✍️✍️✍️
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post