LABARAN WASANNI ARSENAL ZALLAH


Inter Milan na da kwarin gwiwar sayen dan wasan Arsenal Alexandre Lacazette, a cewar rahotanni daga Italiya, ta hanyar Metro.

Dan wasan mai shekaru 30 yana da sauran watanni 12 a kwantiraginsa da Gunners kuma zai iya barin kulob din kyauta a bazara mai zuwa.

Sai dai kuma Inter ta ce tana sha'awar sayen Lacazette a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu kuma tana da kwarin gwiwar kammala siyan dan wasan, dan kasar Faransa


: Bukayo Saka shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa Ingila kwallaye a raga tun bayan Wayne Rooney a 2004 😍 ⚽️ 


 Kevin Campbell ya bukaci fitaccen dan wasan Arsenal Folarin Balogun da ya nemi damar Tafiya aro zuwa wata kungiyar

Kevin Campbell ya bukaci matashin dan wasan Arsenal Folarin Balogun da ya tafi a matsayin aro domin yana bukatar Karin kwarewa  ta hanyar buga manyan wasannin kwallon kafa akai -akai.

Dan wasan mai shekaru 20 yana gab da barin kulob din na Arewacin London a watan Janairu amma ya gamsu da ci gaba kungiyar Hakan yasa ya Kara  rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar Mikel Arteta.

Tsohon Dan Wasan Arsenal' 

Ian Wright ya yi imanin "dole wani abu ya faru" tare da yanayin Raheem Sterling a Manchester City yayin da ake alakanta shi da komawa  Arsenal.


An alakanta Sterling sosai da komawar Gunners a cikin makwannin da suka gabata, tare da takaita lokacin wasansa a City a kakar wasa ta bana - kuma yanzu Wright yana magana da ITV game da abin da ke bukatar faruwa ga dan wasan na Ingila.


Ya ce: "Kuna kallon dan wasa wanda acikin sauki yana daya daga cikin manyan 'yan wasan mu na [Ingila] wadanda ba sa wasa a kulob din sa, a wani mataki dole ne ya warware shi.zuwa wani lokaci


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post