KUNGIYAR KWALLO KAFA TA ARSENAL ZATA WARE WASU MANYAN KUDI AKAN WANI DAN WASA

Kungiyar Kwallo kafa ta  Arsenal zata ware zunzutun kudi  €60m akan tauraron dan Wasa Dan kasar Holland mai shekaru 21aduniya
 
Orkun Kokcu har yanzu yana akan Tsarin Arsenal. Kulob din na Ingila bai manta da dan wasan dan kasar Holland ba, wanda ke da darajar Yuro miliyan 60. Za su gabatar da tayin gabanin kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara.mai zuwa

Kokcu wanda ya Fito  daga kulob din na kasar Holland daga kungiyar matasa, Kokarin sa da Kuma jajircewar sa ta sa har sai da ya kai tawagar farko ta kungiyar, yana da kwantaragi har zuwa Yuni 2025. Duka dukae, ya buga wasanni 111 ya zura kwallaye 16 kuma ya ba da taimako 18.
Gunners, a cewar ‘TalkSport’, suna son dan wasan tsakiyar mai shekara 21 ya karfafa kungiyar a kakar wasa mai zuwa, ya zuwa yanzu a kakar wasa ta bana, ya buga wasanni 33 a fafatawa 21 daga cikinsu a gasar lig din kasar Holland Eredivisie kuma ya zura kwallaye biyar. ne


Wani Rahoto da kafar yada labarai ta kasar Ingila, a yanzu kulob din na Ingila yana shirya tayin mai ban sha’awa don siyan shi a karshen kakar wasan nan. An bayar da rahoton cewa Kokcu yana da darajar kusan Yuro miliyan 60. Koma dai Mai zai faru lokaci ne kawai zai Tabbatar da Hakan  Yan wasa da yawa ana alakanta su da Zuwa Arsenal 

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post