YADDA LASHE GASAR F.ACUP TA SAMO ASALI A TARIHIN ARSENAL




Arsenal 3-2 Manchester United

An buga wasan karshe na cin kofin FA na shekarar 1979 a  rana (12 ga Mayu) a filin wasa na Wembley. Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin mafi girma wasa da aka taba yi a gasar cin kofin FA, 

 Arsenal tana  cin 2-0 a rabin lokaci ta hannun Brian Talbot da Frank Stapleton.

Sai dau a minti na 86 Gordon McQueen ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, sannan bayan mintuna biyu Sammy McIlroy ya mayar da wasan 2-2

Yayin da wasan ke shirin tafiya kara lokaci, murnan da United take yi bai dade ba, inda Alan Sunderland ya zura kwallo a minti na karshe, wanda hakan ya sa Arsenal ta tashi 3-2 Manchester United.

Ana kiran wannan wasan a matsayin "Ƙarshe na minti biyar".

Kofin FA na 1979 shi ne babban kofi daya tilo da Arsenal ta lashe a tsawon shekaru bakwai na jagorancin Terry Neill, wanda aka nada a shekarar 1976 bayan Bertie Mee ya yi ritaya. An kore shi a shekarar 1983.

Haka kuma ita ce kofin karshe da Manchester United ta samu a karkashin jagorancin Dave Sexton, wanda aka nada a matsayin koci a shekarar 1977 kuma ya ci gaba da zama a can har zuwa 1981 lokacin da aka kore shi bayan ya kasa kawo wani babban kofi a kungiyar.


Ibrahim musa funtua

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post