BENJAMIN SESKO:
Labaran da suke fitowa na yau da kullun)
"Abu mafi mahimmanci ga Benjamin Sesko shine yanke shawara da farko ko ya karɓi shawarar RB Leipzig na tsawaita kwantaragi da kungiyar inda zai samu ƙarin albashi.
Dole ne ya gaya musu yadda yake ji kafin Euro, da kuma shawara zai zauna ya tsawaita ko kuma zai bar kungiyar ya gwada kwarewar shi a wani club din
Chelsea, Man United da Arsenal sun gabatar da sha'awarsu akan shi,kuma dukkanin kungiyoyin uku suna jiran jin ta bakin Benjamin Sesko.
Dukkan su suna da ayyuka daban-daban, ra'ayoyi daban-daban, hangen nesa daban-daban da kuma tsare-tsare daban-daban da kuma shawarwari daban-daban ta fuskar albashi.
Zan iya ba ku tabbacin cewa, ya zuwa yau, Benjamin Sesko har yanzu bai yanke shawarar inda zai je ba, inji Fabrizio Romano amma yana da wasu masu tuntuɓar kungiyoyin don fahimtar ayyukan su kuma zai yanke shawara a cikin muhimman kwanaki masu zuwa."