ARSENAL TA RABU DA MAITSARON RAGAR TA


Karl Hein ya koma Real Valladolid ta La Liga a matsayin aro na kakar 2024/25.

Golan mai shekaru 22 ya zo kungiyar Arsenal ne, a cikin 2018 daga kulob din garinsu, Nomme United. Karl ya sanya hannu kan yarjejeniyar Æ™wararrun sa ta farko tare  da club din Arsenal  a cikin Mayu 2019 kuma ya ci gaba da sanya hannu kan sabuwar kwangilarsa ta dogon lokaci jim kaÉ—an kafin ya shiga Reading Amatsayin aro a cikin Janairu 2022, don karasa ragowar wasanni 

Dan wasan na kasar Estonia, Karl ya riga ya buga wa kasarsa manyan wasanni  30. Ya taka rawar gani da kuma aiki mai ban sha'awa inda ya zama Estonia's Young Player of the Year a watan Disamba 2021.

Karl ya buga wasansa na farko a filin wasa na Emirates a watan Satumbar 2022, a gasar cin kofin Carabao zagaye na uku da Brighton & Hove Albion.

A cikin nasararsa ta farkon kakar 2024/25, Karl ya fito a dukkan wasannin da Arsenal ta buga Amurka guda uku da Bournemouth, Manchester United da Liverpool. 

Kowa a Arsenal yana yiwa Karl fatan alheri a kakar wasa mai zuwa tare da Real Valladolid.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post