EMILIANO BUENDIA!!
Labari yana karfi akan maganar zuwan Emiliano Buendia Kungiyar Arsenal.
Dan wasan wadda Arsenal ta dade tana zawarcinsa yana taka leda ne a kungiyar kwallon kafa ta Norwich City dake kasar England. Emiliano Buendia Dan kasar Argentina ne mai shekaru 22. Yana cikin manyan yan wasan Norwich City wadda suka taimakawa kungiyar ta hauro gasar Primier League a wannan kakar wasan da aka kare din. Benudia ya taka muhimmiyar rawa wurin dawowar Norwich City gasar Primier League inda yaci Kwallaye (Scoring) goma sha biyar (15) ya kuma bada (Assits) goma sha bakwai anci (17).
Kungiyar Arsenal ta nemi dan wasan tun a watan Janairu na wannan shekarar sai dai alokacin Norwich City taki amincewa ta saidawa Arsenal da dan wasan, sakamakon suna son haurowa gasar Primier League. Wadda hakan yasanya Arsenal Suka karbi aron Marting Odegard daga kungiyar Real Madrid. Tundaga wannan lokacin Arsenal sukaci gaba da bibiyar dan wasan har zuwa karshen wannan kakar wasan. Sai dai wasu suna ganin Arsenal sunfi maida hankalinsu ne akan Odegard inda suke fatan Real Madrid ta sai da masu da dan wasan. Wata jarida ta ruwaito cewar Arsenal zasu sai Benudia ne kawai idan har basu sami Odegard ba.
Domin samun labaran baya👇👇
Sai dai kungiyar Aston Villa na kokarin ganin tariga Arsenal dauke Dan wasan wadda kudinsa zai kai £40m.
Ganin Aston Vill na kokarin dauke dan wasan yasa kungiyar Arsenal tafara tuntubar wakilin (Agent) din dan wasan dan ganin tayi maza ta dauke shi.
Sabon Darektan wasanni na Arsenal wadda zai yi aiki atare da Edu wato Richard Garlic yayi maza yafara tuntubar wakilin (Agent) Buendia dan kar Aston Villa tarigasu siyan dan wasan.
Shahararren dan jaridar nan wato Fabrizio Romano yace hakika Arsenal sunmaida hankalinsu wurin ganin sun saye Emiliano Buendia. Mahukunta Arsenal sun yaba da yanayin yadda yaron yake taka leda kuma harma sunfara tattaunawa da wakilan dan wasan.
Shima emiliano Buendia ashirye yake da ya amsa tayin zuwa Arsenal. A wata hira da dan wasan yayi da jaridar (#diarioas) yace kowana dan wasa zai yi mafarkin taka leda a babban matsayi kuma a babban kungiya dake ƙasar England ko Spain.
Beundia: Babban abuna kuma mai muhimmanci ace kungiyoyi suna nemanka hakan yana nufin kana kokari kenan, kuma hakan zai karama kwarin guiwa da zaisa kasake kwazo harzuwa lokacin da zaka cimma burinka.
Karka wuce baka shiga 👇👇👇
Idan har Arsenal tasami nasarar dauke Emiliano Buendia to abune mai wahalar gaske ta sai Odegard.
Zuwa yanzu dai alamu yana nuna cewa Arsenal sun maida hankalinsu ne akan Suga sunfara kawo Emiliano Buendia.
Ko dayake Mikel Arteta yace zasu jira suji shawaran Real Madrid akan Odegard.
Ra'ayin Prince Tije.
Nafi bukatar asiyo Odegard akan Emiliano Buendia.
Kudanna nan👇👇👇
Sabida Odegard ya'iya ball kuma a duniyar kwallon kafa yanzu yan wasa masu salon wasan Odegard suna wahalar samu.
Domin salon wasansa yayi iri daya dana Ozil. Ya'iya bada kwallo aci yana iya rike ball.
Sannan salon wasansa zai dace da Arsenal.
Amma zanso naji daga gareku.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije