KIERAN TIERNEY YA BAYYANA HALIN DA YASHIGA BAYAN YASAMI RAUNI

KIERAN TIERNEY YA BAYYANA HALIN DA YASHIGA BAYAN DA YASAMI RAUNI A WASAN LIVERPOOL!

Matashin dan wasan bayan Arsenal dan kasar Scotland wato Kieran Tierney ya bayyana halin da yashiga bayan da yasami rauni a karawar da Arsenal tayi da kungiyar Liverpool a wasan da Arsenal din tayi rashin nasara a hannun Liverpool daci 3-0.
Kushiga ku karanta 👇 👇👇
Dan wasan bayan  wadda Arsenal tasiyo daga kungiyar Celtic a shekarar 2018 akan kudi £27m ya kasance jigo daga cikin tawagar yan wasan Arsenal sakamakon gudunmawar da dan wasan ke badawa .

Dan wasan dan kasar Scotland yayi fama da rauni tun bayan da yazo kungiyar Arsenal inda yayi ta samun rauni har wasu sunfara kallonsa amatsayin dan wasa mai laulayi (Injury Prone) 
Tierney wadda yasami rauni a kokon guiwarsa a karawar da Liverpool ta doke Arsenal a gasar Primier League yace yayi tunanin shikenan tashi ta kare a wannan kakar wasan.

Kieran Tierney:  Lokacin da naji nasami damuwa a kokon guiwata, tuni sai naji araina babu dadi, sai nafara tunanin shikenan bazan sake wasa a wannan kakar wasan ba?
Kudanna nan 👇👇👇
Nasamu matuka na tsawon lokaci. Musamman yadda kungiyata ta Arsenal ke fuskantar wasan kusa da karshe (Semi Final) na gasar Europa league kuma banason ace banbuga wannan wasan ba musamman yadda wannan wasan shine zai tabbatar da kakar wasanmu takare ko muna da sauran tafiya?

Bayan nan nafara tunanin kasata Scotland domin ana tunkarar gasar nahiyar Turai ne (Euros) akwai wasanni da yawa da Yakamata na doka.

Raunin yafaru acikin dan karamin lokaci sai naji nafara jindadin jikina,  hakan yasa sai nakoma sansanin tawagar yan wasan kwallon kafa na kasar Scotland wadda awurin nasami natsuwa. 
 Ina cikin jira naji bayani daga bakin likitan kashi na kungiyar Arsenal wato  Jordan Reece bayan kamar kwana uku zuwa hudu haka sai nasami labari mai dadi daga Jordan Reece cewa bana bukatar tiyata amma zanyi jinya na makonnin shida. Sai Yagayamin zanje gasar Nahiyar Turai (Euros) Dan haka na kwnatar da hankali na. Karna damu kaina akan hakan,  duk da haka abin bakin ciki ne domin bazan taimaki kungiyata a wasu wasanni ba. Amma duk da haka idan natuna bazanyi dogon jinya ba inajin dadi a raina.
Domin samun labaran baya 👇👇👇
Nagode Allah da baza'ayi min tiyata ba. Nadawo taka leda acikin makonni biyar , abinda banyi tunani zai faru ba. Amma  a yanzu inajina da lafiya kuma ashirye nake dan tunkarar gasar nahiyar Turai (Euros).  Ina jina da karfi kuma ina matukar shaukin zuwa gasar nahiyar Turai.

Naji dadin da nasake haduwa da abokan wasana na kasar Scotland kuma zamuyi iya kokarin mu a wannan gasar da za'afara a wata mai zuwa.
Tierney! Inaganin kamar ina samun raunine sakamakon salon yadda nake wasana.  Bazan kalli hakan ba, abin badaga gareni bane.  Bana kallon kaina amatsayin wani babban dan wasa, ina daya da kowana dan wasa a filin daukar horo. Nasan babu dalilin da zaisa nafi kowana dan wasa baiwa, Amma duk baiwar da nake da'ita to ina amfani da'ita sosae. Kuma ina aiki tukuru.
Kaji dan wasa mai kishi muna tare dakai Tierney domin nikaina naji azuciyata da ace kana da lafiya mukayi wasan Villareal da abune mai wahala bamu ciresu ba. Amma haka Allah ya yatsara lamarin babu yadda muka iya. Inafatan zaka haskaka a gasar nahiyar Turai, kuma ina fatan Aka dawo a kakar wasa mai zuwa da karfinka dan taimakawa kungiyar Arsenal. Scotland tana daya daga cikin kasashen da zan dinga kallon wasansu sabida naga wata irin gudunmawar zaka bawa kasarka.

Inama fatan kabuga wannan gasar lafiya kamar yadda kazaku kabuga toh Allah yasa kabuga a sa'a babu rauni. Fatan nasara Kidena Tierney.

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.

Naku 
Admin
Prince Tije


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post