Kungiyar kwallon kafa ta Ath Madrid bata bukatar siyan dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Eruguay wato Lucas Torreira. Dan wasan wadda yayi zaman aro (Loan) na kakar wasa daya da kungiyar Ath Madrid Arsenal zasu yanke shawara akansa bayan gama gasar kofin Nahiyar America (Copa American). Torreira Yana cikin jerin yan wasan da Arsenal ke fatan saidawa a wannan kakar wasan.Shima dan wasan yanuna sha'awarsa na ficewa daga kungiyar Arsenal zuwa kungiyar Boca junior dake kasar Argentina.
Matashin dan wasan bayan Arsenal dan kasar France wato William Saliba zaidawo kungiyar bayan kammala zaman aronsa (Loan) a kungiyar Nice dake kasar France.Dan wasan zaidawo Arsenal a watan bakwai (July) na wanann shekarar alokacin fara wasanni share fage inda za'a bawa dan wasan dama dan yanuna kansa. Ana saran Saliba shine wadda zai maye gurbin David Luiz wadda yabar kungiyar a karshen wannan kakar wasan.
Kushiga nan 👇👇👇
Arsenal bazasu tura dan wasan aro (Loan) a wata kungiyar ba a wanan kakar wasan. Zasu barshi a kungiyar dan bashi dama sugani.
Kungiyar kwallon kafa ta Marsielle dake kasar France naci gaba da tattaunawa da kungiyar Arsenal wurin ganin ta dauke matashi dan wasan Arsenal din dan kasar France wato Matteo Guendouzi. Sai dai haryanxu ba'acimma matsaya tsakanin kungiyoyin biyu ba.
Kungiyar As Roma dake kasar Italiya Sun matsa wurin ganin sun dauke dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Sweezerland wato Granit Zhaka. Arsenal sun sanyawa dan wasan kudi £25m akan shine abinda As Roma zata biya kafin ta'iya siyan dan wasan. Kungiyar As Roma suna duba yiwuwar biyan wadannan kudade da Arsenal ke bukata akan dan wasan.
Kocin kungiyar New Castle United wato Steve Bruce yanuna bukatarsa nason maido da matashin dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar England wato Jeo Willock kungiyar bayan da dan wasan ya kammala zaman aro (Loan) a kungiyar. Joe Willock ya haskaka sosae a kungiyar bayan da yaci Kwallaye takwas a da kungiyar a gasar Primier League. Wadda hakan shine dalilin da yasa kungiyar ta New Castle keson siyan dan wasan. Arsenal zata dawo da Joe Willock tabashi dama a wasanni share fage (pre-season) daga nan ne zata yanke hukunci akan dan wasan. Wasu rahotonni nacewa idan har new Castle United ko wata kungiya ta kawo kudin da yakai £20m akan dan wasan to Arsenal zasu duba tayin amma kasa da £15m toh bazasuma saurari kungiyar ba. Hakan yana nufin idan har kungiyar ta New Castle nada bukatar daukar dan wasan to dole ne sukawo tayin da yakai £20m.
Kungiyar Arsenal tana duba yiwuwar sanya wani dan wasa acikin cinikayyar Emiliano Beundia. Arsenal tana da bukatar daukar dan wasan amma haryanzu kungiyar ta Arsenal basukaiwa kungiyar ta Norwich City tayi ba. Kungiyar ta Norwich City sunyiwa dan wasa kudi £35m -£40m sai dai Arsenal bazasu Sai wani dan wasa ba har sai sunfara saida nasu tukuna.
Kushiga kugani 👇👇👇
Arsenal dai sunfi bukatar dan wasan tsakiyar Real Madrid wato Marting Odegard akan Emiliano Buendia inda haryanzu suna sauraron suji daga kungiyar Real Madrid ko zasu saida masu da Odegard.
Gaskiya Arsenal zasuyi baban kuskure matukar suka saida Zhaka a £25m to wannan babban kuskure ne, domin bazasu iya samun dan wasa irin Zhaka a kudi kasa da £40m ba. A karshe sai dai suje su dauki aron wani dan wasa ko ace su Elneny za'abar maku su. Idan har Zhaka zai kai £35-£40m to hakan dai dai ne, domin anmoreshi dai dai gwargwado. Amma ace dan wasa kamar Zhaka asaidashi £40m wannan ba karamin kuskure bane.
Click nan👇👇👇
Jikina yafara sanyi da harkan wannan transfer nafara jin tsoron kada mutanen nan su yaudaremu domin naga abubuwan sunfara zamowa shirme tun kafin tafiyar tayi nisa. Amma akwai sauran lokaci zamuci gaba da bibiyarsu muga abinda zaifaru.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa
Naku
Admin
Prince Tije