WANI BABBAN DAN WASAN ARSENAL ZAI BAR KUNGIYAR NAN DA WASU KWANAKI MASU ZUWA!!

Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Brazil mai shekaru Talatin da uku (33) wato Willian zai bar kungiyar Arsenal.
Dan wasan wadda yazo Arsenal daga kungiyar Chelsea a farkon kakar wasannan wasa a matsayin aro zai bar Arsenal ne bayan da yakasa tabuka abin azo agani.
Kushiga nan 👇👇👇
Arsenal ta dauki Willian ne daga Chelsea a matsayin kyauta (Free) inda ya kulla yarjejeniya shekaru uku (3) da Arsenal. Sai dai dan wasan baiyi wani abin azo agani ba a kungiyar. Willian yabuga wasanni ashirin da biyar yaci kwallo daya tak. Hakan yasa Arsenal zasu rabu da dan wasan musamman ganin yadda yake dauka albashi mai yawan gaske.

Zuwa yanzu dai ba'asan kowana kungiya dan wasan zai koma ba. Sai dai wasu jaridu suna alakanta dan wasan da komawa kungiyar Chelsea. 

Zuwa yanzu dai Willian bai fara tattaunawa da wata kungiya dake kasar England ba. 
Kudanna nan👇👇👇
A kwanakin baya antambayi Mikel Arteta a wani hira da yayi da yan jaridu akan dagaske Willian zai bar kungiyar Arsenal? Sai Arteta yabada amsa dacewa yana da sauran kwantaragin shekaru biyu damu dan haka yana nan a Arsenal babu inda zaije.

To Amma a yau ta tabbata cewa Willian zai bar kungiyar Arsenal nan da wasu kwanaki masu zuwa.Sai dai haryanxu bamu saniba ko Arsenal din zasu saida dan wasan ne ko ko zasu sallame shi ne kawai ganin bada kudi suka kawoshi ba.

Naji dadin wannan labari sabida ko bakomai yanzu  araina nafara tunanin kila kungiyar Arsenal zasuyi gyara a wannan kakar wasa mai zuwa din. 
Kushiga kugani 👇👇👇
Sabida yadda naga suke kokarin rabuwa da yan wasan da basu kokari a kungiyar. 
David Luiz Out
Bellarin Out
Willian Out
Nkethia Out
Torreira Out
Guendouzi Out
Kolasinac Out
Willock Loan
Maithland Niles Loan

Zuwa yanzu wadannan yan wasan sune wadda tabbas zasu bar kungiyar Arsenal.

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.

Naku
Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post