GUENDOUZI YA JEFAWA ARSENAL BAKAR MAGANA!!
Matashin dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar France wato Matteo Guendouzi yajefi kungiyar Arsenal da bakaken maganganu a shafinsa na twitter bayan da yataya tsohon Kocin Arsenal unai Emery murna lashe gasar Europa league da yayi a daren jiya.
Guendouzi yasami damuwa ne da kungiyar Arsenal a kakar wasa da tawuce na 2019/2020 alokacin wasan Arsenal da Brighton wadda Arsenal tayi rashin nasara daci 2-1 a hannun Brighton din.
Kushiga cikinnan 👇👇👇
Guendouzi ya shaki wuyar dan wasan gaban kungiyar Brighton ne wato Neil Mauphy bayan da aka tashi daga wasan.
Neil Mauphy shine yaci kwallo ta biyu wadda yabawa Brighton nasarar doke Arsenal a wasan, sannan ya doki Leno a kafa harya janyo Leno yayi dogon jinya. Bayan tashi daga wasanne Mauphy yafara ihu yana murnar nasarar da suka samu akan Arsenal sai Guendouzi ya tunkareshi yace masa wahalalle nawa ake biyanka? Wannan magana tayi zafi da yawa har takai ga hukumomin kwallon kafa na gasar Primier League sukayi zama akan Guendouzi amma daga karshe dai basu hukuntashi ba. Hakan yasa kungiyar Arsenal takira Guendouzi zama akan sununa masa kuskurensa akan abinda yagayawa Mauphy wadda hakan yasabawa dokar kwallon kafa.
Acikin wadda akayi zaman dasu akwai Mike Arteta, Edu, da David Luiz.
Guendouzi yaki amincewa dacewa abinda yayi kuskure ne, yana kafa hujja dacewa yayiwa Mauphy hakanne sabida haushin abinda yayiwa Leno.
A karshe dai Antashi a zaman batare da Guendouzi ya amince da yayi laifi ba. Hakan yasa Arteta ya dakatar dashi daga zuwa filin atisaye na Arsenal.
Kudanna nan👇👇
Wasu rahotonni sunce David Luiz yabi Guendouzi har gida akan yabawa Arteta da Edu hakuri shikuma yace sam tunda baiyi laifi ba bazai basu hakuri ba.
Wannan shine sanadiyar samun damuwar Guendouzi da kungiyar Arsenal har takai ga Anturashi zaman aro a kungiyar Hartha Berlin dake kasar Germany. Bayan da tsohon Kocin Arsenal wato Unai Emery yayi nasarar daukar kofin gasar Europa league a daren jiya Geudouzi yataya tsohon Kocin nasa murna a shafinsa na twitter inda yayi wasu kalamai da'ake ganin kamar cin fuskane ga kungiyar tasa ta Arsenal.
Unai Emery shine wadda yakawo Guendouzi Arsenal Yakuma bashi dama sosae. Wadda kusan yana cikin dalilan da yasa magoya bayan kungiyar Arsenal suka tsani Unai Emery sakamakon yana ajiye manyan yan wasan kungiyar irinsu Ozil yana amfani da Guendouzi wadda a wannan lokacin yaro ne karami bai kamata ace yana buga kowana wasa a Arsenal ba. Musamman ganin yadda karfinsa bai kai ba.Akwai kyakkyawar Fahimta tsakanin Guendouzi da Unai Emery wadda hakan shiyasa Guendouzi ya taya Unai Emery murnan lashe gasar Europa da yayi.
Matteo Guendouzi: kyak'kyawar Tafiya, haka kwallon kafa take, Mutum mai basira sannan da baiwa. Kacika mafarkin Babban birni wannan kungiya, dama kowa acikin kungiyar, sannan mafarkin magoya bayan wannan kungiyar yazama gaskiya.
Ka aikata hakan, kasan yadda ake cin kofuna (Trophies)! Girmamawa ga Unai Emery.
Dan samun tsoffin labaranmu👇👇👇
Kazo kadaukeni.. 👈 Alamar wasa.
Wanann shine sakon da Guendouzi ya rubuta a shafinsa na twitter dan taya tsohon kocinsa Unai Emery murnan nansar daukar kofin Europa league.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije