Vieira ya sake yin magana Game da siyan Arsenal

Shahararren dan wasan nan na Arsenal, Patrick Vieira ya yi kira ga masu kungiyar, dangin Kroenke, da su ‘bar kulob din Nan Haka  ya tafi kuma ya Kara da cewa wanda ya kafa kamfanin Spotify, Daniel Ek ba zai yi kasa a gwiwa ba a yunkurin sa na sayen Arsenal din.daga Gurin kroenke

Shahararren attajirin dan kasar Sweden yayi magan a makon da ya gabata cewa mamalakin Arsenal Kroenkes -   da dansa Josh, wanda darakta ne a kulob din - sun ki amincewa da tayin da aka yi masu na sallamar da kungiyar wanda ake ganin zai  kai fam biliyan 1.7.

http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/05/lucas-torreira-ya-fito-ya-fadi-gaskiya.html

Vieira, tare da Thierry Henry da Dennis Bergkamp, ​​suna ta taimakawa Ek da kudirin sa na siyen Arsenal kuma yanzu ya bukaci Kroenkes da ko dai su ‘kara shiga tsakanin Dan Ganin Ansamu Gyara ko kuma su yarda da tayin da yayi masu, su tafi. Su bar kungiyar

'A cikin shekaru biyu da suka gabata na yi imani cewa kulob din bai dauki alkibla mai kyau ba. Kuma ina ganin lokaci yayi da za'a canza. Idan canjin bai faru ba, na yi imanin cewa Arsenal za ta shiga tsaka mai wuya, 'Vieira ya fada wa ITV Football Podcast.

'Zamu iya yin hukunci ne kawai daga waje. Muna kallon kowane wasa a Arsenal kuma yana da wahala a gane kungiyar da muka Buga wasa a baya.

'Yana da wahala a fahimci dalilan da suka sa Arsenal ta sauka daga Matsayin ta Acikin  shekaru biyun da suka gabata amma a bayyane Abun yake  ta rasa Arsene Wenger  kuma ba Har yanzu ba'a sami irin ma'aikatan da suka da ce da irin Tsarin  Arsene. Wenger 

‘Kuma ina ganin duk shekara Arsenal ta Gaza  tsallakawa  zuwa Kofin Zakarun Turai ko ma dai  Europa League. Din da take zuwa Don haka wannan babban abin takaici ne a garemu baki daya a matsayinmu na masoyan Arsenal.

‘Amma mun isa lokacin da kowa a kulob din, yake Bukatar yaga Ansamu Gyara sosai  Kroenkes Yana da damar da   shiga tsakani don mayar da Arsenal  kungiyar da zata Dace da lokacin da Ake ciki

'Idan kuwa ba haka ba, ina ganin lokaci ya yi da za su bar kulob din ya tafi su bar wani ya kula da kungiyar kwallon kafa.'

Na tabbatar da Ek zai dawo da sabon tayin, Nan Gaba kadan  Vieira ya ci: ‘Tabbas zai sake gwadawa.ko za'a Dace su sallama Mai kungiyar

'Ya kasance a can na dogon lokaci. Shi mai kishin Arsenal ne. Nayi magana da shi sau biyu da sha'awar sa da sadaukarwar sa ga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zai kasance abin birgewa.sosai Ga kowa da kowa

http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/05/arsenal-sunfara-tattaunawa-da-wakilin.html

‘A bayyane yake, idan kungiyar ba ta sayarwa ba ce babu abin da zai iya yi amma zai kasance a can kuma zai jira  yana son sayen kungiyar.

‘Ina ganin zai zama da gaske ne saboda Arsenal na cikin wani mawuyacin lokaci. A wurina, lokaci ne da ya dace ya yi iyakan kokarinsa ko kuma ya yi abin da zai iya siyan kulob din, don daidaita kungiyar’

http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/05/sakon-cedric-soares-ga-magoya-bayan.html

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post