SAKON CEDRIC GA MAGOYA BAYAN KUNGIYAR ARSENAL!!
Dan wasan bayan kungiyar Arsenal Dan kasar Portugal Cedric Saoures ya aikawa magoya bayan kungiyar Arsenal da sako ta shafinsa na Twitter. Dan wasan wadda yazo Arsenal daga kungiyar kwallon kafa ta Southampton a shekarar da ta gaba baisami buga wasa yadda Yakamata a kungiyar ba. Amma duk da haka yanuna goyon bayansa ga kungiyar ta Arsenal.
Cedric: Kakar wasa mai wahalar gaske yazo karshe. Bamu kare kakar wasan a matsayin da kungiyar Arsenal yadace ta kasance ba sannan rashin magoya bayanmu (Fans) a wasu wasanni shine abu mafi wahala agaremu a wannan kakar wasan.
Kushiga cikin nan👇👇
Dan wasan yakara dacewa ina tunanin rashinku a tare damu ya bayyana yadda kuke da matukar muhimmanci agaremu dama kwallon kafa baki daya.
Zanci gaba da maida hankali dari bisa dari ga wannan kungiyar, Ina da tabbacin zamu cimma bukatunmu atare nan bada jimawa ba.Ina godiya ga kowa da kowa bisa soyayyarku agareni, Inafatan sake garinku nan bada jimawa ba.
A kwanakin baya Kocin kasar Portugal ya gayyaci Cedric wasan neman gurbin zuwa kofin duniya (World Cup) a wannan lokacin dan wasan yafara haskakawa sabida damar da yake samu na buga wasanni a Arsenal. Sai dai tundaga wannan lokacinne Kocin Arsenal Mikel Arteta yakoma ajiyeshi a bench wadda hakan yayi sanadiyar Kocin Portugal bai sanya sunan dan wasan acikin wadanda zasu wakilci kasar Portugal a gasar nahiyar Turai da za'afara a wata mai zuwa ba.
Ku danna wannan 👇👇👇
Kasancewar Cedric Yana da shekaru 29 ayanzu kuna ga Yakamata a bashi dama da yaci gaba da taka leda a Arsenal ko a sai dashi? Musamman ganin yadda Cullum Chambers yake kokari a nomba biyu.
Wanann shine abinda dan wasan ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije