Labarin Wasanni masu Qayatarwa
Kungiyoyi Chelsea da Borussia Dortmund na tattaunawa domin Ciniki dan wasan gaba na ingila da yake Buga Wasa kungiyar Chalsea Tammy Abraham, mai shekara 23, da kuma dan wasan tsakiya Callum Hudson-Odoi, mai shekara 20.
Wannan wani labari ne maras dadi ga kungiyar West Ham, wacce da wuya ta iya biyan farashin da Chelsean ta sanya wa Abraham din Na fan miliyan 40.
Haka kuma yunkurin da Dortmund ke yi na sayen Hudson-Odoi ka iya bude kofa ga dan wasan gaba na Ingila Jadon Sancho,mai shekara 21,da Yake Wasa kasar Germany ya bar kungiyar ta Jamus zuwa Manchester United.
Dan wasan gaba na gefe dan Brazil Raphinha,mai shekara 24, y ace bay a tunanin barin Leeds United, duk da rade-radin da ake yin a danganta shi da tafiya Manchester United ko Liverpool. Inji (Jaridar Metro)
A yanzu ta tabbata cewa dole ne kungiyoyin Premier su jira har zuwa watan Yuli kafin su tunkari Barcelona a kan cinikin dan wasan gaba na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28. Rahotanni na cewa Arsenal da Everton na sha'awarsa siyan shi inji . (Sky Sports)
Antonio Conte ya dauki kofin gasar Itlaiya da Juventus da na Premier da Chelsea yanzu kuma ya kara daukar na Italiya da Inter Milan
Kociyan Lazio Simone Inzaghi ne ake ganin watakila zai maye gurbin Conte a Zakarun a kungiyar Inta Milan ta Italiya. Inji (Sky Sports)
Mai tsaron raga dan Ingila Sam Johnstone, mai shekara 28, ya ce makomarsa na hannun West Brom duk da danganta shi da tafiya Leeds ko Wes Ham da ake yi a kan fam miliyan 20
Har yanzu Real Madrid ba ta yanke shawara a kan ko ta zata siyar da dan wasan tsakiya ta dan kasar Norway Martin Odegaard,mai shekara 22, wanda ya yi zaman Aro daga January a kungiyar Arsenal.
Arsenal na sha'awar dan wasan Leverkusen Edmond Tapsoba, yayin da kulob din na Bundesliga ke neman dan wasan da Mikel Arteta ya kora daga kungiyar a kakar da ta gabata 👀👀👀
Bayer Leverkusen na zawarcin dan wasan bayan Arsenal William Saliba
http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/05/unai-emery-ya-aike-wa-arsenal-da-sako.html
Dan wasan baya na Arsenal William Saliba ya zama dan wasan da kungiyar Bayer Leverkusen ta ke son sayowa a lokacin bazarar, in ji rahotanni a Jamus.
Saliba, mai shekara 20, an sayo shi daga Saint-Etienne a shekarar 2019 a yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 27 amma har yanzu bai buga wasan farko da Gunners ba.
http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/05/wani-babban-dan-wasan-arsenal-zai-bar.html