Juventus ta tabbatar da ta korar Andre Pirlo daga horar da kungiyar, bayan ya jagoranci kungiyar na tsahon kakar wasa daya. Pirlo wadda tsohon dan wasane ga kungiyar ta Junventus yazama Kocin kungiyar ne bayan da Sarri yabar kungiyar. Sai da Pirlo yakasa tabuka abun azo agani a kungiyar ta Junventus inda yakare kakar wasan Seria A a mataki na 4. Sannan Fc Porto tacireshi a gasar zakarun Turai. Hakan yasa Juventus ta sallami Pirlo din. Ta kuma maye gurbinsa da Tsohon kocinta wato Manuel Allegrini.
Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sun rubuta saƙon bankwana ga Coach Zidane a shafinsu na sada zumunta. Sai dai ance tsohon dan wasan Chelsea wato Eddern Hazard da kuma Isco su kaɗaine basuce komiba haryazu. Ko hakan yana nuna suna da wata matsala ne da shi ko dai jinkirtawa Suka yi lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan. Zidane wadda yadawo Real Madrid a karo na biyu yabar kungiyar ne bayan da takasa cin wani kofi a wannan kakar wasan.
Kushiga nan 👇👇👇
Real Madrid sunfara tat'taunawa da wasu daga cikin masu aikin horaswa da suka hada da Pochettino, Conte da tsohon Kocin kasar Germany wato Joachim Low.
David De Gea ya gaza ture fanareti ko Daya acikin cikin shekaru 5. Jimillar Anbuga Mai Guda 40 Amma ko Daya Bai iya turawa ba. Wannan shi ake cewa Rariya. Ina yan jan gida kuzo kuji abin kunyar da dan wasanku yayi.
Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta tuntubi Tsohon Mai Horarwa da kungiyar tasu wato Mauricio Pochettino a kan komawarsa kungiyar. Pochettino dai yabar kungiyar Totteham ne a kakar shekarar da ta gabata bayan da kungiyar tashiga cikin wani hali. Sai dai haryanxu kungiyar bata dawo ganiyarta ba duk da korar da suka masa hakan yasa suke neman yadawo. Ahalin yanzu dai Pochettino yana horas da kungiyar Psg ne dake kasar France, sai dai wasu rahotonni na nuna cewa Kocin zai iya barin kungiyar ta Psg bayan da yakasa lashe gasar kasar na League 1.
Domin samun labaran baya 👇👇👇
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta # Gabon # Guélor Kanga Kaku zai Gurfana Gaban kwamitin ladabtarwar na kwallon kafa na #African don bayyana dalilin da yasa mahaifiyarsa ta mutu a shekarar 1985 amma shi An haifeshi 1990 ... 🙆♂️🙆♀️
Takardun sa sun nuna mahaifiyarsa ta mutu a shekarar 1985. 👀
Yanzu haka dan wasan ya shirya domin fuskantar kwamitin #CAF domin yayi bayanin dalilin da yasa aka haifeshi shekaru 5 bayan rasuwar mahaifiyarsa. Chakwakiya kenan zamu cigaba da bibiya da Kuma sauran lokacin da za'a zaman da Kuma bayanin da zai bayar
Matsalar kudi ce zata Tilastawa Inter Milan siyar da wasu Yan Wasan Hakan Ne yasa Ake cigaba da Alakanta kungiyar Arsenal da neman Achraf Hakimi, wanda za a iya sayar da shi don dai daita Abinda kungiyar take Bukata a wannan bazarar
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Psg suna neman dan wasan suma wadda haka babban kalubale ne ga kungiyar Arsenal.
Hakimi yakoma Inter Milan ne daga Kungiyar Real Madrid a kakar wasa da ta gabata a kan kudi £36m.
Kungiyar kwallon kafa ta : AC Milan ta sayi Mike Maignan daga kungiyar Lille akan kudin da ya Kai kusan £13m dan wasan ya sanya hannu Akan yarjijeniya kwantaragi har zuwa watan Yuni 2026.
Hakan yake Tabbatar da kungiyar ta
Lille yanzu ta rasa mai horarwa da mai tsaron raga na kungiyar da ta lashe kofin. France
Tsohon Mai Horar da kungiyar Chelsea Antonio Conte, wanda ya bar Inter Milan ranar Laraba ya fara nuna sha'awar zuwa kungiyar, Tottenham. Dake kasar ingila
Tottenham na duba yiwuwar kawo Conte, amma ta fara sanya ido akan Zidane. Tsohon coach Real Madrid
Ana sa ran za a nada Simone Inzaghi a matsayin sabon Mai Horar da Inter bayan ya bar Lazio da aiki. (Athletic
Za a nada tsohon shugaban kungiyar Sheffield United Chris Wilder a matsayin sabon Mai Horar da kungiyar West Brom.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Wasanni acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Rabi'u MDC