DAN WASAN DA YAFI KOWA YAWAN ASISTS A ARSENAL DA DAN WASAN BAYA DA YAFI KOWA YAWAN ASISTS!!

Zanci gaba da kawo tarihin Arsenal kamar yadda nayi alkawari. 


Dan wasan da yafi kowa yawan buga wasa a Arsenal shine  David O'Leary yabuga wasanni  (698)


Ya buga primier league sau (558)
Fa Cup (70)
Carling Cup (70)

                  CAESAR JENKYS

Caesar Jenkyns shine dan wasan Arsenal na farko a tarihi da yafara bugawa kasarsa wasa. Ya buga wasan Wales da Scotland a ranar  21/3/1896.

Jimmy Ashcroft shine dan wasan Arsenal na farko da yafara taka leda a kungiyar kwallon kafa ta kasar England wato (The Tree Lions) ya buga wasane a ranar 17/2/1906 inda England sukayi wasa da kasar  Ireland.



                 THIERRY HENRY

Shine dan wasan Arsenal da yafi kowa samun gayyata daga kasarsa dan buga mata wasa.  Thierry Henry ya wakilci france a wasanni (81) ya buga wasanni (78) babu wani dan wasan Arsenal da ya taba bugawa kasarsa wasa har (78) sai Henry.

Kenny Sansom shne dan wasan Arsena da yafi kowa yawan bugawa England wasa.
Ya buga wasa England wasanni (77).


                         THEO WALCOTT

Theo walcott shine matashin dan wasan Arsenal na farko a tarihin kungiyar da England suka  gayyatarsa dan ya bugawa kasar wasa yana da  Shekaru 17 da kwana 75 a duniya. A wasan England da Hungry wadda akayi a ranar 30/5/2006.

Shine dan wasan Arsenal mai karanci shekaru da ya fara samun katin gayyata daga England.


Kushiga nan 👇👇


                         DAVID JACK

David Jack shine dan wasan Arsenal da yaci kwallaye 14 a jare.

Dan wasan ya zura har kwallaye 14 acikin raga a wasanni tara na gasar First Devision (Primier League) da ya buga a jere daga ranar 24/10/1931 zuwa ranar 19/12/1931.


                      IAN WRIGHT

Ian Wright shine dan wasan da yafi kowa yawan kwallaye a fitowa a wasa (Appearance) dan wasan yaci kwallaye (16) a wasanni (9) da aka fara wasa dashi. Ma'ana wasan da yake cikin Firt Eleven. 15/9/1994/ zuwa 23/11/1994.


                        THIERRY HENRY

Henry shine dan wasan da yafi kowa yawan zura kwallaye a tarihin Arsenal.
Henry yasha kwallaye 228 a kungiyar Arsenal. Henry ya doke Ian Wright wadda dama shi ke rike da wannan kambun,  inda shi Wright ya zura kwallaye 185. Ya karya wannan tarihin na Wright ne a October 2005 a wasan da Arsenal ta buga da Sparta Parague a gasar Champion League.

#HENRY shine dan wasan da yafi kowa yawan taimakawa (Asists) A tarihin Arsenal.

Kushiga nan 👇👇

#HENRY yayi Asists har (80) a kungiyar Arsenal wadda hakan yasa ya zarce kowa.


#HENRY Shine dan wasan Arsenal da yafi kowa yawan jefa kwallaye a zare a gasar Primier League. Inda ya sha kwallaye (175) a gasar Primier League.

#HENRY Shine dan wasan da yafi kowa yawan Hatricks (shan kwallaye 3) a Arsenal.
Yayi hatricks sau (8)

#HENRY Shine dan wasan da yafi kowa yawan shan  Penalty a Arsenal. 

Ya buga Penalty guda 22 inda yabuga guda 15  a filin wasan Arsenal (Home) guda 7 a wajje (Away).


#HENRY Shine dan wasan Arsenal da yafara cin kwallaye da suka kai 30 a kakar wasa daya na gasar Primier league a shekarar 2003.
Sai dai a 2011 Robin Van Persie shima ya zura kwallaye a suka kai 30.


                     TED DRAKE

Drake shine dan wasan Arsenal da yaci kwallaye 44 a kakar wasa daya a shekarar 1934-1935
Haryanzu  babu wani dan wasan da ya karya wannan tarihin.

Kudanna nan👇👇

#DRAKE shine dan wasan yaci kwallaye 7 a wasa daya a ranar 14/12/1935 yaci Aston villa ne wadnnan kwallayen.

                      PATRICK VIERA


Viera shine dan wasan Arsenal da yafi kowa samun katin Horo (Red Card)

Viera yasami Red Card har sau (8)

#VIERA  shine dan wasan Arsenal da yafi kowa samun katin Gargadi (YELLOW CARD)  ya sami yellow Card sau (75) ya sami yellow Card guda (32) a gidan Arsenal (Home) yasami guda (43) a wajje (Away).

Jack Wilshere shine dan wasan Arsenal na farko da yafara fitowa a First Eleven a gasar Primier League yana da kanaun shearu. 16years  256Days.


#FABREGAS: shine matashin dan wasan Arsenal  na farko da yafara cin kwallo a gasar Primier League yana dak kananun shekaru 17years 114days.

Kutaba nan 👇👇


#FABREGAS: Shine dan wasan Arsenal da ya fara cin kwallo yana da kananun shekaru. 16years 212days. Ma'ana babu wani matashin dan wasa a Arsenal da yaci kwallo a first team a kowana gasa yana shekara 16 sai Fabregas. Ya kafa wannan tarihinne a ranar 2/12/2003 akan Wolves.

#FABREGAS: Shine dan wasan Arsenal da yafara fitowa acikin First Eleven yana da kananun shekaru. 16years 177days a wasan Arsenal da Notherham United a ranar 28/10/2003. A gasar Carling Cup (Carabao Cup)


#BERGKAMP  shine dan wasan Arsenal da yaci kwallo a gasar Primier league yana da manyan shekaru. 36years 332days.


#JOHN RADFORD shine dan wasan Arsenal da yayi hatricks (Cin kwallae 3 a wasa daya) yana da kananun shekaru. 17yrs 315days. Ya kafa wannan tarihin ne akan Wolves a shekara 1965 a gasar First Devision.

#JOCK RUTHERFORD  shine dan wasan Arsenal da yayi hatricks yana da manyan shekaru. 39years  352days ya kafa wannan tarihinne akan Shefield United  a ranar 20/9/1924 a gasar first Devision.

Kushig nan 👇👇


#JOCK RUTHERFORD Shine dan wasan Arsenal da yafito acikin first Eleven yana da manyan Shekaru. 41years 159days. A wasan Arsenal da man united a ranar 20/3/1926.


#KOSCIENLY shine dan wasan bayan Arsenal da yafi yawan zura kwallaye a zare. Dan wasan ya zura kwallaye (15)
Ya kafa wannan tarihin ne ranar 13/4/2016 a wasan Arsenal da Westham United.



#BELLARIN shine dan wasan bayan Arsenal da yafi kowa yawan Asists a gasar Primier league a kungiyar.

Bellarin yayi  asists 2 a wasan Arsenal da shefield United wadda aka buga ranar 4/10/2020. 

Bellarin yayi Asists (20) a gasar Primier league. 


                       MESUT OZIL


#OZIL Shine dan wasan Arsenal da yafara yin Asists 50 acikin dan karamin lokaci a gasar primier leageu.

Ozil ya kafa wannan tarihinne ranar 11/3/2018  a wasan Arsenal da Watfod.

Ozil ya karya record din Eric Cantona ne wadda yayi Asists 50 a wasani 143.
Shkuma Ozil yayi Asists 50 a wasanni 141.



        PIERRE EMERICK AUBAMEYANG


Aubameyang shine dan wasan Arsenal da yafara cin kwalaye 50 a gasar primier league acikin dan karamin lokaci.

Dan wasan yaci kwallaye 50 ne a wasanni 79 da yabuga na gasar Primier League. 



Ackin wadanan tarihin wana tarihi ne kuke ganin za'ayi saurin karyashi?





Admin
Prince tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post