ARSENAL NA NEMAN SCOTLAND TABASU TIERNEY!
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal suna son Scotland ta basu Tierney.
Ankillace matashin dan wasan ne akan zarginsa da ake na yin mu'amala da Stuart Amstrong wadd yake dauke da kwayar cutar nan ta Covid19.
Duk da kasancewar anyiwa Tierney gwajin Cutar har sau 3 amma ba'a sameshi da cutar ba kasar tashi ta scotland sunce sai yayi kwana 14 yana killace. Wadda hakan zai sa dan wasan bazai buga karawar da kungiyarsa ta Arsenal zatayi da Manchester City ba a ranar asabar.
Amma bisa dukkan alamun yana nuna cewa dan wasan zai iya buga wasan Arsenal da man city din.
Kocin Celtic Neil Lenon wadda shine tsohon kocin Tierney yace dan wasan zai sami buga wasan Arsenal da man city.
Shiga kabin dake ciki 👇👇👇
Suma kungiyar ta Arsenal sunce suna da kwarin guiwar akan zasu iya karban dan wasan dan yabuga wasan Arsenal da man city. Sai dai ba'aga dan wasan cikin hotuna yan wasan Arsenal da sukayi atisaye na ranar jumma'a ba.
Tsohon kocin Arsenal wato Arsen Wenger ya bayyana yadda Cecs Fabregas yaso yadawo kungiyar Arsenal a 2014.
Fabregas dae yabar Arsenal ne a 2011 inda yakoma kungiyar kwallon kafa ta Bacerlona. Amma a 2014 ya nuna sha'awarsa nason dawowa kungiyar Arsenal. Sai da Wenger yanuna masa baya bukatarsa awannan lokaci.
Wenger yace naki amincewa da yadawo ne sabida na nunawa saura yan wasan Arsenal dake kungiyar wadanda suke ganin zasu iya haskakawa a wata kungiyar idan sunbar Arsenal dan hakan yazama darasi ga yan baya.
Ku dannan nan 👇👇
A kwanaki wenger yace a 2015 ma Van Persie yakirani akan yanaso yadawo Arsenal amma naki amincewa dashi domin alokacin ma shekarunsa sunja.
Wenger yace yasan cewa yadawo da wasu yan wasa Arsenal bayan suntashi irinsu Henry, Campbell, jens Lehman. Amma kanana yara da suka barmu bazanyi hakan ba.
Kocin Manchester City wato Pep Guardiola ya tabbatar da dan wasan tsakiyar kungiyar dan kasar Belgium wato Kelvin De Bruyne yasami rauni wadda hakan yayi sanadiyar dan wasan bazai iya buga wasan da kungiyar zatayi da Arsenal ba a gasar primier league mako na 5.
Guardiola yace tabbas dan wasan yasami rauni kuma bazai iya buga wasan Arsenal ba, amma dai raunin bamai muni bane.
Guardiola yakara dacewa Gabriel Jesus ma bazai buga wasan ba, duk da kasancewar raunin dan wasan bawani mai girma bane bazamuyi kasadar sashi a wannan wasan ba.
Guardiola yace sai dai akwai yiwuwar Sergio Aguero ya buga wannan wasa.
Aguero wadda ya shafe watanni 3 yana jinya yadawo daukar horo tun mako biyu da suka gabata. Kocin na man City yace zamuyi atisaye gobe da safe daga nan ne zamu yanke shawaran ko zai buga wasan ko bazai buga ba.
Pep Guardiola ya yabawa tsohon abokin aikinshi wato Mikel Arteta wadda shne kocin kungiyar Arsenal a yanzu.
Guardiola yace tabbas yana da kwarewar da zai'iya kawo chanji a kungiyar Arsenal. Sannan zai iya dawowa kungiyar da martabanta. Ina matukar farin ciki akan kokarin da yake yi a London.
Matashin dan wasan bayan Arsenal wato Willian Saliba zai ci gaba da zama a kungiyar Arsenal zuwa january.
Arsenal sun so bada aron (Loan) din dan wasanne zuwa wata kungiya inda zai sami isas'shen wasanni. Sai dai hakan baiyiwu ba.
Kushiga cikin nan 👇👇
Arsenal dai basu saka sunan Saliba cikin yan wasan da zasu buga masu wasan Europa League ba, sabida tunanin dan wasan zai iya barin kugiyar. To kasancewar daga yau duk wata maganar Tranafer ta kare, zamu ga koh dan wasan zaisami shiga cikin wadda zasu buga wa kungiyar gasar primier league? Ko turashi under23 za'ayi ? Kasancewar dai dama dan wasan yabuga wanna gasar sau daya a wannan kakar wasan.
Ranar monday ne dai (19/10/2020) kowata kungiya dake gasar Primier league zata mikawa Hukomomin primier league sunayen yawan wasanta wadda zasu buga mata wannan gasar.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran wasanni cikin harshen hausa.
Admin
Prince Tije