Gabriel yazama gwarzon dan wasan Arsenal na watan Satumba!!
Sabon dan wasan bayan kungiyar Arsenal dan kasar Brazil wato Gabriel Mangalheas wadda Arsenal tasiyo a wannan kakar wasan daga kungiyar kwallon kafa ta Lille dake kasar France akan kudi €27m an zabeshi amatsayin gwarzon dan wasan Arsenal na watan Satumba (Player Of The Month). Dan wasan wadda yabuga wasanni 4 cikin wasanni shida da kungiyar ta buga yasami kyautar Man Of The Match har sau 2 acikin wasanni hudun da ya buga.
Dan wasan yabuga wasa 3 a gasar primier league inda yasami kyautar Man of The Match a wasan Da Arsenal suka buga da Fulham da kuma Westham United. Sannan yabuga wasa daya a gasar Caraboa Cup.
Edward Nkethia ya kafa tarihi a england.
Matashin dan wasan gaban Arsenal dan kasar England wato Nkethia yazama dan wasa na farko a tarihin kasar England daya zura kwallaye 14 a Under 21 na kasar England wato Young Lions.
Dan wasan yakafa wannan tarihin ne a jiya bayan da kungiyar tasa ta Young Lions ta doke Turkey under21 daci 2-1 a daren jiya.
Nkethia wadda shine ya jagoranci kungiyar ta Young Lions (Captain) yasami damar jefa kwallo daya araga wadda wannan kwallo itace tabashi damar kafa wannan tarihin inda ya karya tsohon tarihin Alan Shearer wadda dama shi ke rike da wannan tarihi na zura kwallaye har 13.
Nkethia yasami kyautar man Of the match a wannan wasa inda aka zabeshi amatsayin dan wasan da yafi kowa kokari a cikin yan wasan da suka taka leda a wannan wasan.
Matashin dan wasan Arsenal dan kasar Brazill yace yanzu yafara samun lafiya da kwarin guiwa. Dan wasan yace yanz nafara jin lafiya a guiwar kafata, Bayan samun wannan raunin naji tsoron tilastawa kaina akan dan fara atisaye. Amma yanzu haka naji sauki sosae, nan da dan wani lokaci zanfara atisaye da kwallo.
Martinelli yace muna da yan'wasa masu kyau tare da Coach mai tunani mai kyau, da son ayi nasara. Muna wasa mai kyau, atisaye mai kyau, kowanmu yanason nasara zamuyi iya kokarinmu dan ganin muncimma burinmu.
Wannan kakar wasa ce mai matukar muhimmanci agaremu, mun dauki kofuna a kakar wasa da tagabata, haka zamuyi kokari muga munsake daukowa a wannan kakar wasan, sannan musami damar buga wasan Champion a shekara mai zuwa.
Martinelli yace nayi matukar farin ciki da zuwan Willian da Gabriel kungiyar. Abin farin ciki ne kasami yan kasarka wadda suke jin yaren da kakeyi a kungiyar da kake. Dama akwai David Luiz a kungiyar wadda nariga na shaku dashi. Yanzu kuma ga Willian da Gabriel duk da bamu dade da haduwa dasu ba amma zan'iya cewa mutane masu kirki. Kuma ashirye suke da subawa wanna kungiya gudunmawarsu.
Dan wasan ya bayyana hakanne awani hira da akayi dashi.
Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Egypt wato Mohammed Elneny ya yabawa kocin Arsenal mikel Arteta.
Dan wasan wadda aka turashi zaman aro (Loan) a kungiyar Besiktas a kakar wasan data gabata. Yadawo Arsenal ne gabatowar fara wannan kakar wasan.
Sai dai da farkon dawowar dan wasan anyi tunanin za'asaida shi amma bayan haskakawar da yayi a wasan karshe (final) na kofin Community Shield da Arsenal suka buga da Liverpool da kuma wasan Fulham sai yasa kocin na Arsenal mikel Arteta ya sauya ra'ayinsa na son saida dan wasan.
#Elneny yashaidawa Arsena Digital. Kafin dawowata bankira Mikel Arteta ba, nayi ta tunanin mezai faru idan nadawo.
Bayan munzauna da Arteta sai nagaya masa yadda yake bada Horo, da yanayin yadda yakeso adinga buga wasa, sannan ina matukar son yadda muke atisaye yanzu. Arteta yana bawa kungiyar nan gudunmawa sosae, wadda hakan yasa nayi farin ciki kuma ashirye nake da na taimakawa kungiyar.
#Elneny Alokacin Unai Emery bana buga wasa sosae, wadda hakan yasa narasa kwarin guiwa buga wasa. Shiyasa da naje Besiktas ina samun isas'shen wasa sai kwarin guiwata yadawo. Ko da nadawo Arsenal kowa yayi farin ciki da dawowata kungiyar.
Nasami kwarin guiwa a filin atisaye domin abokan wasana kowa yana zuwa yace min #Mo kwarin guiwarka yadawo kana wasa mai kyau yanzu. Zanci gaba da gina wannan kwarin guiwar tare da koyan sabbin abubuwa.
Kullum da safe idan natashi ina tunanin ya zankoyi sabbin abubuwa, wannan shine yake raina a kullum hakan yasa ina tashi da safe nakan je nayi atisaye dan tahakanne kawai zan koyi sabbin abubuwa.
Idan har Elneny ya dore ahakan zai zama kamar sabon signing da Arsenal.
Aex Runar Runnarson ya yabawa Arsenal.
Matashin dan wasan wadda yazo Arsenal daga kungyar kwallon kafa ta Dijon Fc dake kasar France akan kudi €1m yace yayi matukar farin ciki da Arsenal suka dauko Thomas Partey daga Ath Madrid.
Matashin mai tsaron ragar ya kasance masoyin Arsenal ne tun yana yaro.
Alex yace siyo Partey da Arsenal tayi ba karamin abin farin ciki bane. Kuma hakan zai Tabbatar wa duk wani masoyin Arsenal da yanzu kungiyar ta dauki hanyar gyara.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.
Admin
Prince Tije.