Thomas Partey yazo Arsenal ne daga kungiyar Ath Madrid akan kudi €45m.
Dan wasan dan kasar Ghana mai shekaru 27 yazo Arsenal ne daren ranar Monday da ya gabata. A ranar Talata kuma dan wasan yawuce zuwa kasar Turkiya (Turkey) inda yasami tawagar kwallo kafa ta kasar Ghana domin buga wasan sada zumunci da kasar ta Ghana tayi da kasashe biyu wadda suka hada Mali da Qatar.
Hakan yasa Arsenal bata sami damar yiwa dan wasan hotuna da kuma yin hira dshi ba.
Sai yau talata dan wasan yadawo dawo London inda akayi masa hotuna tare da yin hira dashi.
Acikin Hiran da akayi da dan wasan ya aikawa Arteta da sakon cewa shifa ashirye yake.
Ga dai cikak'ken abinda dan wasan yace.
Dan jarida akan zuwanka Arsenal?
Kushiga nan 👇👇
Thomas Partey: Ba karamin abin farin ciki bane, lokacin da wakili na (Agent) dina yakirani a waya ya gayamin cewa Arsenal zasu biya kudina nayi matukar farin ciki. Nakasa bacci a wannan rana sabida farin cik. Duk da kasancewar haryanzu banfara wasa a Arsenal ba, amma sakon da nake samu daga magoya bayan Arsenal ba kadan bane. Magoya bayan Arsenal suna matukar son (Jindadi) zuwa n kungiyar.
Dan Jarida mezaka ce akan Arsenal?
Thomas Partey: Arsenal kungiyace da nadade ina bibiyarta tun ina karamin yaro. Lokacin muna yara muna kallon wasani sosae, a shekarar 2004 da kungiyar tayi Unbeatean ba karamin kyau suke dashi ba. A wannan shekaran ne suka saye zuciyoyi mutane.
Kushiga nan 👇👇
Dan wasan yaci gaba da bayyana Arsenal amatsayin daya daga cikin manyan kungiyoyi a duniya. Inda yace kungiyar ta cancanci tasami manyan nasarori a duniya, sai dai ayanzu basu samin wadanan nasarorin. Zamuyi iya kokarinmu wurin ganin mundawo dawowa da kungiyar martabanta.
Dan wasan yakara dacewa sakonni da magoya bayan Arsenal suka dinga tura masa nacewa Dan Allah Partey kaxo Arsenal ko muki yin bacci abin farin ciki ne agareshi. Sabida hakan yasa yayi matukar farin ciki da zuwansa kugiyar, dan yanzu haka yanajin kungiar tamkar acikin iylansa yake.
Mezaka ce akan wasan man city ?
Thomas Partey: Ina son buga babban wasa kwarai dagaske. Amma hakan yadanganta ga shawaran da kocinmu da kocinmu zai yanke ne akaina ko zai fara wasa dani ko bazai fara ba, sai abinda ya yanke.
Kushiga cikin nan 👇👇
Dan wasan yace yana da bukatar yayi atisaye da abokan wasansa tukuna sai yaga abinda zai faru.
Kamar dai yadda nagaya muku ne sai shawaran da Coach din ya yanke akaina. Duk da kasancewar yanzu nazo amma ashirye nake. Sai dai ina bukatar nakoya salon wasan kungiyar.
Zanyi kokari naga nakoya duk wani irin salon wasan kungiyar cikin dan karamin lokaci, kuma zan tabbatar nayi dukkan abinda ake bukata a filin atisaye dan mikel Arteta ya ganewa idonsa ashirye nake da nayi masa wasa.
Dan wasan yakara dacewa... Nasan haryanzu ina da bukatar nakara gyara wasana, sannan akwai abubuwan da zan koya da wannan sabuwar kungiyar tawa, wadda ta hakane zan cimma burina dama burin kungiyar.
Inajin wannan wani sabon kalubale ne arayuwata. Inason nasami wani dabara da wannan kungiya da tazama tamkar family dina. Ashirye nake da nabada dukkan wani taimako da zan'iya dan dawo da martaban wannan kungiya.
Ina kallon gasar Primier League sosae tun ina kasar ghana, yawancin abokaina yan Ghana suna kallon wannan gasar sosae.
Wannan wani kalubale ne agareni. Ina matukar son nayi wasa a Babbar gasa Kuma yanzu nasami wannan damar domin kuwa gasar primier league na daya daga cikin manyan gasa a duniya. Dan haka ina farin ciki dana kasance anan (Arsenal)
Dan jarida ko kana ga zaku iya lashe gasar primer League?
Thomas Partey: Wannan shine daya daga cikin Ajandarmu, Ajandar kungiyar, nima shine ajandata. Ya kamata mudawo da kungiyar mazauninta (Cin kofunan) munsan cin kofuna abune mai wahala amma zamuyi iya kokarinmu akan hakan.
Wanan shine abinda dan wasan yace cikin hiran da akayi dashi dazu.
Muna fatan Arteta zai fara wasa dashi Asabar ganin dan wasan ba karamin dan wasa bane da za'ace wannan wasan yayi masa girma.
Gobe laraba ne dai Thomas Partey zai fara daukar horo da kungiyar Arsenal.
A yanzu haka matasan kungiyar kwallon kafa (Under21) na England suna wasa da kasar Turkey under21. Idan har Nkethia yasami nasarar jefa kwallo daya zai kasance dan wasa na farko a tarihin kasar England da yaci kwallaye 14 a kungiyar kwallon kafa na matasan England wato Young Lions.
Kushiga nan 👇👇
Alan Shearer shine wadda ke rike da wannan kambun tarihin inda yake da kwallaye 13.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.
Admin
Prince Tije.