TARIHIN KUNGIYAR KWALLON KAFA TA ARSENAL!!

Ankafa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar 1886.

Ankafa kungiyar ne ta hannu wasu ma'aika wani ma'aikata da ake kira Dial Square  a wani wuri mai suna Royal Arsenal. Ana kiran wurin da sunan Arsenal ne sabida wurine da ake ajiye makamai awani yanki na Woolwhich a kasar England.
Ana kiran kungiyar dasuna Royal Arsenal a wannan lokacin. Kungiyar takasance karkashin jagoranci wani dan kasar Scotland mai suna David Danskin wadda shine yafara siyawa kungiyar kwallo (Football)

Dial Square ko muce Royal Arsenal sunfara buga wasane ranar 11/10/1886 a wani wasan sada zumunci da sukayi da kungiyar Eastern Wenderers na bikin bude fiin wasansu. Kungiyar ta Dial Square (Royal Arsenal) sunyi nasara daci 6-0.


Bayan yan wasu kwanaki ne sai kungiyar ta cire sunanta na Dial Square tabar Royal Arsenal.  Ana cikin haka sai kungiyar ta Royal Arsenal suka bar filin chanza fili wasa daga  Plumstead Common zuwa Manor Ground a 1888 kenan. Sai dai Royal Arsenal basu dade a wannan filin wasan ba sakamakon filin babu kyau, sannan baida abubuwan da suke bukata. Sai suka koma wani flin wasa kusa da manor Ground ana kiran fili da suna Invicta Ground. Bayan shafe shekaru 3 Royal Arsenal suna taka leda a wannan fili sai suka sake koma tsohon filin su wato manor ground sakamakon Invicta ground yayi masu tsada.


A wanan lokacin Royal Arsenal sun lashe kananun kofuna (Local Trophy) a shekarar 1889-90 Royal Arsenal suka sami damar shiga gasar Fa cu. A wannan lokaci daga gasar Fa cup sai yan wasanni sada zumunci su kadai Arsenal ke bugawa.

A 1893 sai aka chanzawa kungiyar suna zuwa Woolwich Arsenal,  aloakacin sao wata karamar kamfani ta saka hannun jarinta a kungiyar dan nemo kudin da za'agyra filin wasan kungiyar na Manor ground.  A wanan shekarar ne sai aka bawa woolwhich Arsenal damar fara buga second Devision.

Woolwhich Arsenal sunyi shekara 11 suna buga second Devision batare da sunyi wani abun kirki ba.

A  1899 sai aka bawa Harry Bradshaw aikin kungiyar sai ya siyo yan wasa 2 wadda suka hada da jimmy Ashcroft da Jimmy Jackson. A 1903 Harry Bradshaw yayi nasarar hauro da kungiyar zuwa first Devsion. Daganan yabar kungiyar Woolwhich Arsenal yakoma Fulham.

Woolwhich Arsenal sukayi ta fafatawa a first Devison har zuwa 1913 batare da sunyi wani abun kirki ba. Acikin wanna shekarun da suka kwashe suna buga first Devision sau 2 suka taba karewa ana 9.


wannan wani wasane da Woolwhich Arsenal suka buga da New Castle a shekarar 1906.


Haka Woolwhich Arsenal sukaci gaba da rayuwa matsalar tat'talin Arziki ya addabi kungiyar wadda hakan yasa suka saida wasu manyan yan wasansu irin su Jimmy Ashcroft,  Tim Coleman,  da Bert freman.

Ahankali kungiyar tafara durkushewa sabida rashin kudi. Ana cikin haka sai wani mai kudi ana cemasa Sir Henry Norris ya zuba hannun jari a kungiyar yazama shiyafi kowa hannun jari  a kungiyar.

Norris sai yanemi da yahada kungiyar Woolwhich Arsenal da Fulham su zama kungiya sabida shine Chairman na kungiyar Fulham a waccan lokacin.

Amma hukumar kwallo kafa ta England suka ki amincewa.

Norris yafara tunanin yaza'ayi ya farfado da kungiyar Woolwhich. Sai yafara tunanin gina fiin wasa. Yasai fili a wani gari Highbury a arewacin London. 

Norris yakashe makudan kudade wajen gina wannan filin wasan. A karshen kakar wasan 1912-13 Woolwhich Arsenal suka koma wannan sabon filin wasan da aka saa sunan Highbury.
Sai dai a wannan shekarar woolwhich Arsenal suntafi relegation inda suka koma buga second devision.
A 1914 aka cire woolwhich acikin sunan kungiyar aka bar Arsenal.
A 1919 kungiyar suka sake haurowa zuwa first devision. Inda  wasan farkon wannan kakar wasan mutum dubu ashirin da uku (23, 000) suka shiga Highbury dan kallon wasan Arsenal.

Wannan sune tawagar kwallo kafa na Arsenal a kakar wasan 1920-21.

Dawowar Arsenal first devision baizo da armashi ba dan sun kasance basu kokari.
A 1923-24 Arsenal takare gasar First Devision a mataki na 19th wadda maki dayane tsakaninta da fadawa relegation zone. Hakan yasa Norris ya sallami Knighton.

A may 1925 Arsenal ta dauki Herbert Chapman daga Huddersfield amatsayin mai sabon kocin kungiyar.

Chapman yakawo sabbin chanje chanje a kungiyar kama daga formation yanayin daukar horo da sauransu. 

A match 1933 Chapman yasa aka sauya tsarin rigunan wasan Arsenal (Jersey) shne aka kara wannan farin dake jersey ayanxu.

Chapman yakawo sauye sauye da dama a Arsenal. Sai dai  new castle tazo ta wargaza Planing din chapman inda taci 7-0 hakan yasa Chapman yasake sauya formation na kungiyar.


Arsenal tasami nasarar karewa amataki na 2 a gasar first Devision a shekarar chapman na farko a kungiyar.

Sai dai bayan wannan shekarar Arsenal batayi wani abun azo agani ba.

Hakan yasa Chapman yashiga kasuwa yasiyo yan wasa irinsu  joe Hulme,  jack lambert,   horbie Roberts,  Tom Parker.
Chapman yagyara team nashi da wadannan yan wasa. A 1926-27 Arsenal tasami damar zuwa wasan karshe (Final) na fa cup. Sa dai tayi rashin nasara a hannun cardiff city daci 1-0.

Chapman bai hakura ba yasake shiga kasuwa inda yasiyo yan wasa har 4 wadda suka hada da Eddie Hapgood, David Jack,  Alex James,  da Cliff Bastin.

A shekarar 1929-30 Arsenal suka sake zuwa final na fa cup a wannan karon sunje ne da tsohuwar kungiyar Chapman wato Huddersfield. Arsenal sunyi nasara da ci 2-0 Lambert da james ne suka jefawa Arsenal kwallaye a xare.


Wannan nasara na Arsenal yazama shine na farko a tarihin kungiyar da sukaci wani major Trophy.


A 1930-31 Arsenal tsake zuwa final na Fa cup sai dai awannan karon tayi rashin nasara a hannun New Castle daci 2-1.

wannan wani bangarene daga cikin hotunan wasan Arsenal d New Castle a final na fa cup a shekarar 1931-32.


Wannan rashin nasara yataba kungiyar Arsenal matuka. 

Wadda yayi sanadiyar rashin tabuka abin azo agani a faron fara kakar wasan 1932-32. Sai dai a shekaran Arsenal sukaci first devision na farko a tarihin kungiyar inda suka yi nasara akan Aston villa daci 5-0 a filin wasansu na Highbury. Wannn nasara itace tabawa Chapman damar lashe gasar.

Sai dai bayan wannan lokaci manyan yan wasan Chapman irisu  Tom Parker,  David jack. Suka fara nuna gajiya sakamakon girma yafara kamasu.

Hakan yasa Chapman yahauro da George Male senior Team daga second team sannan yasiyo  Ray Bowden.

Daganan Al'amura suka fara lalacewa Chapman inda yayi rashin nasara a hannun Warsall daci 2-0 a gasar Fa cup.yan wasan Arsenal mutum 5 suka samu rauni a wannan wasan.

Wannan rashin nasarar yabatawa Chapman rai sosae sakamakom Warsall suna buga Third Devision ne. Yasa saida  Tommy Black da Charlie walsh.

A kakar wasan 1933-34 Arsenal sunfara kakar wasan da kafar dama. Amma a January 1934 Chapman ya mutu sanadiyat cutar sanyi (Pneumonia) 

Tundaga wannan lokaci Arsenal taci gaba da haskakawa  A kakar wasan 1951-52 Arsenal suka fara wasan kakar da kafar dama inda ake ganin masu zasuci First First devision da fa cup. Sai dai raunin da wasu daga cikin manyan yan wasan Arsenal sukaji yasa Arsenal sunrasa kofunan duka sunyi rashin nasara a hannun man united wadda wannan nasarar shiyabawa man United damar cin kofin first Devision Arsenal sunkare kakar wannan wasa ana 3.  

Sati daya da wannan wasan Arsenal suka buga final Fa Cup da New Castle. Arsenal sunyi gag'gawan fara wannan wasan da wasu yan wasansu dake jinya. Ana fara wasan da minti 35 Walley  Barnes yasami rauni a guiwar kafa sannan a wannan lokaci idan dan wasa yasami rauni ba'achanji hakan yasa yan wasan Arsenal suka koma mutum 10 acikin fili. Arsenal dai sungama wannan wasanne da mutum 7 acikin fili sakamakon raunin da yan wasansu suka samu a wasan. Arsenal dai tayi rashin nasara daci 1-0 a hannun new Castle.

A kakar wasan 1953-54 Arsenal sukaci first Devision karo na 7. Inda suka doke Burnley daci 3-2 wadda wannan nasara itace tabasu damar daukar kofin first Devision na wannan shekara. 

Arsenal dai sun dauki kofinne da tazarar kwallo inda makinsu (Points) yazo daya da Preston North End.



Wenger Era.
A shekarar 1996 Arsenal suka sanar da daukar Arsen weger amatsayin kocin kungiyar.


A wanann lokacinne Arsenal tazama abin kallo a idon duniya 

Wenger yasiyo kawo irinsu Viera,  Pires,  Henry,  wadanda dasune yaci manya nasorori a kungiyar.


Wenger yaci kofuna primier league har sau 3 da kungiyar Arsenal inda daga ciki yaci kofi da akewa lakabi da Unbeatean.


Arsenal dai sunyi wasa arba'in da tara (49) batare da andokesu ko da sau daya ba.

Wadda wannan nasara shine babban tarihin da kungiyar ta'ajiye.

Sannan wannan shne daya daga cikin abubuwan da baza'a taba mantawa da Arsen wenger ba a kungiyar Arsenal.

Wenger ya hada team mai karfin gaske dga 2002 zuwa 2006 inda wanna team har kullum anabada misali dasu a duniyar kwallo kafa.

A shekarar 2006 Arsenal suka kawo karshen zamansu a filin wasa na Highbury inda suka koma sabon fiin wasan da suka gina karkashin jagoranci arsen Wenger.
Ansaka ma wannan fili suna Fly Emirte Stadium.

Wadda haryanzu a wannan  fili Arsenal ke taka leda.



Wannan shine kashi daya na tarihin Arsenal da zan dinga kawo wa .



Kusaurari kashi na biyu na nan tafe.



Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post