ARSENAL TA BAYYANA DAN WASAN GABAN DA TAKE SON DAUKA

Wasu Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayyana dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Red Bull Salzburg Karim Adeyemi a matsayin wanda take zawarcinsa a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara mai zuwa.

Dan wasan mai shekaru 19 ya ja hankalin jama'a daga ko'ina cikin Turai saboda rawar da ya taka a gasar Bundesliga ta Austria zuwa wannan kakar, tare da ra'ayin Liverpool da Paris Saint-Germain.

A yanzu dai Arsenal na son siyan dan wasan na Jamus amma an gaya musu cewa dole ne su jira har zuwa lokacin bazara kafin su kama burinsu.

Dan wasan mai shekaru 19, ya zura kwallaye 11 a wasanni 14 da ya buga a matakin farko da kuma kwallaye uku a wasanni hudu na gasar zakarun turai da ya buga wa kungiyar Salzburg a wannan kakar, inda ya zura kwallaye 25 a raga tare da taimakawa 17 a wasanni 73 Dan Shekara 19 Ana Ganin zai iya Haskawa Acikin kungiyar Arsenal idan yazo


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post