Dan wasan bayan Arsenal Nuno Tavares ya umurci mutane da kada su yi ‘mamakin’ kyakykyawan yanayi da Gunners.take ciki
A halin yanzu dai 'yan wasan Mikel Arteta suna tsakiyar wasa goma ba tare da an doke su ba a dukkanin wasannin da suka buga, inda suka lashe takwas daga ciki.
Wannan kyakkyawan tsari ya sa Gunners ta hau teburin Premier cikin sauri a cikin 'yan makonnin nan. A yanzu sun zama na biyar a matsayi na yanzu bayan sun yi rahin Nasara Wasanni Farko sakamakon shan kashi uku a jere a Farko
Hakan ya kasance wani gagarumin sauyi mai ban sha'awa daga Arsenal, kuma wanda ya ba da mamaki ga wasu masana da magoya bayansa.
Sai dai Tavares, wanda ya koma kungiyar Daga Benfica a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, ya dage cewa salon kulob din ya kamata ya zama al'ada ga kulob mai girman Arsenal kuma ya bayyana burin su na ci gaba da kasancewa a saman tebur.
Da yake magana da talkSPORT, dan wasan mai shekaru 21 ya ce:
"Ban san dalilin da yasa mutane ke mamakin Arsenal ba.
"Mu babban kulob ne kuma muna da 'yan wasa masu kyau. Ban san dalilin da yasa mutane ke mamakin hakan ba. A gare mu, al'ada ne kuma mai sauƙi don cin wasanni da buga wa Arsenal.
Muna cikin biyar na sama.
"A gare mu, muna so mu kai ga na sama don haka ban san dalilin da yasa mutane ke mamakin hakan ba.
"Mu kungiya ce mai kyau kuma mutane suna bukatar su fahimci mu Arsenal ne. Muna bukatar samun nasara a wasanni domin cimma burinmu."
Gunners ba shakka suna fuskantar gwaji mai tsanani na sahihancin su a yau yayin da suke tafiya zuwa Anfield don karawa da Jurgen Klopp na Liverpool.
Idan har ta samu nasara, Arsenal za ta yi sama da Reds a teburin Premier, kuma za ta iya kawo karshen karshen mako da maki uku kacal tsakaninta da Chelsea wadda ke kan tebur a yanzu.
Tavares kuma bai boye burin kulob din na samun maki uku ba.
Ya ci gaba da cewa:
"Wannan wasan yana da girma a gare mu, za mu je Anfield don gwadawa mu ci wasan kuma shi ke nan." Muna Fatan Hakan ya Kasance