ARSENAL NA SHIRIN DAUKAR DAN WASAN GABAN CHELSEA

Arsenal na shirin daukar dan wasan gaba na Chelsea Armando Broja a bazara Mai Zuwa   matashin dan wasan, Mikel Arteta ya ji dadin bajintar da ya yi a matsayin zaman  aro a Southampton a kakar wasa ta bana.

Kocin Arsenal Mikel Arteta yana yin la'akari da Yan wasan da zai dauka a bazara a Daga gurin abokan  hamayyarsa Chelsea a lokacin bazara don neman dan wasan gaba Armando Broja, wanda ke kan gaba Acikin yan Wasan da zai dauka Yana zaman aro a Southampton.

Dan wasan mai shekaru 20 yana zaman aro a St Mary's gaba daya kakar 2021-22 kuma ya zura kwallaye bakwai a wasanni 24 a karkashin Ralph Hasenhuttl.

Yanzu, a cewar Football London, Arteta da Arsenal sun lura Kokarin dan  kudancin Albania  kocin Dan Kasar Sipaniya yana girmama dan wasan gaban sosai.


Arsenal ta yi kokarin sayen dan wasan gaba kuma ta kasa daukar dan wasan a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. Dusan Vlahovic ya kasance babban burinsa amma ya zabi komawa Juventus daga Fiorentina.

Shima Pierre-Emerick Aubameyang ya bar Gunners din a kyauta bayan da Arteta ya kore shi kuma tun daga nan ya koma Barcelona.

Haka kuma, dan wasan gaba na Arsenal Alexandre Lacazette kwantaragi shi zai kare a karshen kakar wasa ta bana.

A halin yanzu suna matsayi na shida a kan teburi amma suna da wasanni biyu da ya Zama kwantai Manchester United a matsayi na biyar da uku a kan West Ham, wadda a halin yanzu take matsayi na hudu. Hammers sun fi na Arteta maki biyu ne kawai.

A sauran wasannin da suka rage, Arsenal za ta fafata da ita domin neman gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na hudu kuma na karshe.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post