Mikel Arteta ya dage cewa sabbin 'yan wasa ba za su yi watsi da damar Zuwa Arsenal ba,
Mikel Arteta ya yi imanin cewa dalilin da zasa 'yan wasan za su ki komawa Arsenal shi ne idan an ba su karin kudi a wani wuri.akan abinda arsenal zata basu
Gunners ta sha fama a kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu inda suka kasa kawo sabon dan wasan gaba.ko daya
Arsenal ta yi tayin sayen dan wasan Serbia Dusan Vlahovic, wanda a karshe ya bar Fiorentina ya koma Juventus a tsakiyar kakar wasa ta bana.
Kulob din ya kuma nemi dan wasan Real Sociedad Alexander Isak da na Everton Dominic Calvert-Lewin amma an Rufe ba tare da sabon dan wasan gaba ba yazo ba duk da tafiyar Pierre-Emerick Aubameyang.
Rahotanni sun ce dan wasan kasar Sweden Isak bai da tabbas akan komawarsa Emirates saboda rashin buga gasar zakarun Turai - tun shekarar 2017 bai buga gasar ba.
Haka kuma ana rade-radin cewa Arsenal na iya bakin kokarinta wajen shawo kan Bukayo Saka ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi idan har ta kasa samun gurbin shiga gasar zakarun turai a kakar wasa mai zuwa.
Amma dangane da ‘yan wasan da ke son shigowa, Arteta ya ce bai taba yin magana da dan wasan da bai son komawa Arsenal ba.
"Muna da al'ada, abin da kulob din ya zaburarwa, abin da muke a matsayin kulob yana da girma," in ji Arteta.