Arsenal vs Wolves
Premier League
Fabrairu 10, 2022 19:45 UK lokaci
TARIHIN HADUWAR SU ...
A wannan makon za a yi karawa ta 119 tsakanin Arsenal da daya daga cikin wadanda suka kafa gasar kwallon kafa ta ingila Wolverhampton Wanderers a dukkan gasa. Gunners ce ke kan gaba a cikin jerin wasanni Arsenal tayi nasara 58 Wolverhampton-32, anyi Canjaras 28 tsakanin haduwar su,
Wasan farko tsakanin club biyu ya zo ne a tsohon filin Manor a Plumstead, lokacin da Woolwich Arsenal ta yi nasara da ci 2-0 a tsohuwar rukunin farko (ba koyaushe ake kiranta "Premier League") a cikin 1904 ba.
Nasara mafi girma -da Arsenal tayi Acikin karawar shine 7-0, 1934 (akan hanyar su ta lashe gasar lig) 1934, Division 1
Wolves: (sau biyu) 6-1 a 1946 da 1959 - duka Division one
Fitattun ‘yan wasan da suka taka leda a kungiyoyin biyu
Eddie Clamp, Bobby Gould, Bob McNab, Alan Sunderland, Oleh Luzhnyi, da Emmanuel Frimpong.
Trivia : Wolves sun kasance ɗaya daga cikin mambobi 12 da suka kafa gasar ƙwallon ƙafa. Za a iya sunan sauran? Babu Man United gaba ba ɗaya, Acikin su