KALAMAN ARTETA AKAN WASAN LIVERPOOL

Mikel Arteta ya gana da  manema labarai akan wasan  Liverpool.


 📍Akan Fuskantar Liverpool

 Zamu fuskanci mafi kyawun a kungiya a gasar Primier League ta Ingil, kuma dole ne mu yi iya kokarinmu don mu doke su.

 Zamu  fuskanci kungiyar da ta mamaye kowane bangare na wasan kwallon kafa Don haka, dole ne mu  kasance cikin mafi kyawun lokaci.

 📍Arteta akan Brendan Rodgers yana kwatanta Ramsdale a matsayin 'mafi kyawun mai tsaron raga na Ingila a yanzu.

 Na godewa Brendan da ya yi tunanin haka. Dole ne Ramsdale ya ɗauki waɗannan kalmomi don kara mashi kwarin gwiwa. Ya kasance na musamman tun ranar da yazo Arsenal.

 📍Shin Ben White shine mafi kyawun dan wasan bayan Ingila a yanzu?

 Ban sani ba, muna matukar farin ciki da yanayin yadda yake taka leda.

 📍Akwai wani shiri na ban mamaki da dabaru da kake shirin yi a gobe?

 Sai gobebn zamu ga mezai faru.

 📍 Matsayin Arsenal a Tebur?

 "Akwai kungiyoyi mafi kyau a gasar Primier League domin shine abinda table din ya nuna,  ba mu yi komai ba tukuna.

 📍Mene ne dalilin kokarin Arsenal a wannan a yanzu?

 Muna wasa mafi kyau, muna da fahimtar abin da muke so. Mun fahimci abinda mukeso muyi,da kuma  matakin da mukeso mukai. Sannan muna da fahimtar juna kuma komai yana tafiya dae dae a yanzu.

 📍Shin wannan shine mafi kyawun lolacinka a kungiyar tun bayan zuwan ka kungiyar?

 Ina tsammanin haka, sabida irin yadda muke sami natsuwa a wasanni mu.cda kuma yadda muke cin wasanni zanciya cewa Eh.

 📍Shin kasancewar ku a na hudu ya fara chanza tunaninka?

 To tabbas hakan zai sanya mu a matsayin da muke fatan ganin munsamu, sannan zamuyi  imanin cewa zamu  iya kasancewa babbar kungiya da zamu goga kafada da manyan kungiyoyin a gasar. amma gaskiyar magana ita ce har yanzu da sauran tafiya.

 📍Shin zai zama rashin nasara a gareka idan har baka kare a mataki na  hudu?

 Ba zan iya tunanin haka ba a yanzu, ina tunanin yau da gobe. Abinda nasani kawai shine na duba teburin gasar ta yadda zai kara karfafa min guiwa. Bazan iya fara duba abinda mukayi a yanzu ba, sabida inaga hakan bazai karfafa min guiwa ba.

 📍Menene abinda zai zama nasarar ka a wannan kakar wasan?

Kara yin nasara a wani wasa a wannan gasar, domin hakan zai karama kwarin guiwa sosae.  Doke mafi kyawun kungiya a wannan gasar  zai kasance wani babban abu a garemu. shine burinmu a gobe.

 

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post