Munajin dadin taka leda takanimu

Martin Ødegaard: Tabbas akwai  wani abu na musamman da ke faruwa a nan yanzu a cikin kungiyarmu. Kowa yana jin hakan ajikinsa.

  Muna gina wani abu na musamman. Tawagar yan wasan ne da muke suke son junanmu, kuma muke jin dadin buga kwallo a tare.

 Martin Ødegaard: Ina ganin ina cikin yanayi mai kyau, amma ina ganin duk abin da ya shafi kungiyar ne - kungiyar tana taka rawar gani sosai, wadda hakan yake  saukaka mana wurin wasa. Kuna ganin  Thomas da Granit, iri aikin da suke yi, wadda hakan yake bani damar yin wasa cikin sauƙi a tsakiyar fili. 

 Martin Ødegaard a kan kwallon da yayi ihu wadda harta janyo akaje   VAR: "Na tabbata da abinda nake fada  gaskiyane, tabbas naga kwallo ta taɓa hannun wani daga cikin yan wasansu sai dae  ban san wanene acikin yan wasan nasu ba, amma na tabbata naga kwallon ta taɓa hannunsa  kawai na ga kwallon ta taɓa hannunsa.  Na yi farin ciki da hukuncin alkalin wasan da ya bamu bugun Penalty, domin wannan nasara ce babba agare mu.

 Martin Ødegaard game da jituwar dake tsakanin magoya bayan Arsenal da kuma yan wasan dake  cikin ƙungiyar. Wannan wani sabon abune agareni. Domin yanayi ne da ban taba samun kaine aciki ba.

Wannan sune kalaman Odegard bayan antashi daga wasan da Arsenal ta doke Liecester City daci 2-0.

Kuna ganin ko Odegard zai iya maye mana gurbin Ozil?

Kuci gaba da kasancewa a tare mu damu dan samun labaran Arsenal cikin harshen Hausa

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post