KALAMAN ARTETA BAYAN WASAN LIECESTER CITY

Mikel Arteta: Kalaman Arteta bayan antashi daga wasan Liecester city.

 Arteta akan mahimmancin farin ciki

 Eh ina ganin haka ya kamata ya kasance, idan 'yan wasan da ke wakiltar kungiyar ba su jindadi  to sai mu je wani waje na daban domin hakan yana nufin muna yin abin da bai dai ba. suna jin dadin zama yan wasa kuma dole ne su ji dadin hakan. 

 Arteta a kan Partey

 Ya kusa zura kwallo a raga daga dukan kwallo da yakeyi kafin a shigo 18. Ya bada gudunmawa adukkan kwallaye biyun. Za ku iya ganin shi ne gwarzon dan wasan watan da ta gabata. Yanzu abin yarage kawai shine yazama duk wasa zaiyi kokari kamar yadda muke tsakanin daga garesa. 

 Arteta ya akan wasan Liverpool

 Wannan wani mataki ne na dabanm Dole ne mu dauki wasan cikin sabon salo. Dole ne mufara yin  shiri a gobe ta yadda za mu iya doke su.

 Arteta a kan Ramsdale

 Ya cire kwallo mai hatsari gaske a lokacin da muke cin 1-0. Irin wannan  lokacin ne kuke buƙatar mai tsaron raga wadda zai iya   fitar da ku daga matsala. 

 Arteta akan ko yana kallon  teburin gasar Primier League a yanzu.

 Ina kallon tebuer tare da wasannin da suka rage. Dole ne mu sa ido mu shirya don wasa na gaba. Ni ba  babban dan wasan caca ba ne, ballatana nace wani abu akan table din.

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal aciki. Harshen Hausa.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post