KALAMAN ARTETA AKAN WASU ABUBUWA

Mikel Arteta Akan maganar kwantaragi Bukayo Saka!!

Ina da kwarin guiwa akan cewa mu da wakilan Bukayo Saka duk muna da kwarin guiwa akan dan wasan zai sanya hannu a sabon kwantiragi. Yanzu Abinda yarage kawai shine mu tabbatar da hakan a takarda. Ina son mu kammala komai sabida kar maganar ta dinga dauke mana hankali.

Arteta akan Fabio Viera.

Sakamakon yana iya buga wurare (Positions) da yawa hakan wani Abu da ya janyo hankalinmu akansa sannan munyi imanin zai bamu zabuka masu yawa. Dangantakarsa da Amiru Rowe wurin buga wurare ma banganta zata zama mai karfin gaske.

Arteta akan rade-radin da ake yi akan Pepe zai bar Arsenal.

Mun tattauna akan hakan sabida yan wasan damu dasu acikin tawagar suna da yawa, dan haka zamu kyale wasu yan wasan su tafi inda sukeso. Daga yanzu zuwa a rufe kasuwar musanye yan wasa komai zai iya faruwa.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post