Arsenal na son dauko dan wasan Wolves Pedro Neto kuma sun yi magana da wakilinsa Jorge Mendes sama da wata guda.
Ana kallon dan wasan na Portugal mai shekaru 22 a matsayin wanda zai maye gurbin Nicolas Pepe wanda zai iya komawa Nice a matsayin aro.
Neto ya koma Wolves daga Lazio shekaru uku da suka gabata kuma ya kasance babban jigo a kungiyar farko karkashin Nuno Espirito Santo da Bruno Lage.
Ya zuwa yau, ya buga wasanni 95 a Molineux, inda ya taimaka 12 kuma ya zira kwallaye 11. Kafin ya koma Ingila, ya zo cikin matsayi a Braga kuma ya shafe kakar wasa a matsayin aro a Lazio.
A kakar wasan da ta wuce, ya buga mafi yawan kwallon kafa a matsayin dan wasan gefen hagu amma kuma ya taka leda a dama, a matsayin dan wasan tsakiya mai kai hari da kuma dan wasan gaba. Ainihin, yana da Ζ™warewa wanda da alama ce ta, ta irin dan wasan da Arteta yake dauka a Yanzu Wanda zai iya buga gurare da dama acikin fili
Tun da farko a lokacin bazara, Arsenal ta shirya kashe kusan fam miliyan 45 don siyan Raphinha kafin Barcelona ta shigo cikin Cinikin ta dauke shi,
agent' na dan wasan Mendes ya taka rawa gani wajen kawo Fabio Vieira zuwa Arsenal - har yanzu Akwai tunanin cewa wannan yarjejeniya zata iya yin Wahala wajan shawo kan kungiyarsa sabo da mahimmanci da yake shi ,
kuma Wolves suna cikin matsayi mai Ζ™arfi don ganin sun taka rawar gani
Arteta yayi magana a fili game da sha'awarsa na "Ζ™ara yan wasa"
Admin
Rabi'u Umar