MAKOMAR NICLOAS PEPE

Tat'taunawa na tafiya yadda Yakamata tsakanin Arsenal da OGC Nice akan dan wasan gefen Arsenal Nicolas Pepe.

Pepe zai koma ƙungiyar OGC Nice a matsayin aro na kakar wasa daya. 

Yanzu haka ana tattaunawa ne akan Albashin dan wasan wadda OGC Nice zasu biya. Ma'ana dae Arsenal zasu bawa Kungiyar aron Pepe Amma sune zasu dinga biyan Pepe albashi bawai Arsenal ba. Pedro Neto Yana cikin jerin yan wasan da Arsenal ke nema dan maye gurbin Pepe. Sai dai a yanzu Arsenal sun maida hankali ne wurin ganin sun sallami Pepe tukuna.

Source: [Fabrizio Romano]

Edu Gaspar ya zabi ya bada aron Nicole Pepe be akan ya siyar da dan wasan. Sabida a yanzu idan akace za'a siyar da Pepe to tabbas asarar za'ayi domin kuwa babu wadda zasu sayi dan wasan da daraja. Amma idan aka bada aronsa yaje yayi kokari to a kakar wasa mai zuwa darajarsa zata daga a wannan lokacin za'ayi iya samun wadanda zasu siyo shi da daraja.  Dan haka da zarar Pepe yabar Arsenal to mu shiryawa zuwan dan wasan gefe.

✍️✍️✍️
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post