Matashin dan wasan gefen Wolves dan kasar Portugal wato Pedro Neto yana son komawa kungiyar Arsenal sai dai bazai takura dole akan sai bar kungiyar Wolves ba.
Arsenal dai na kokarin neman dan wasan gefe da zai maye gurbin Nicolas Pepe wadda zai koma ƙungiyar OGC Nice a matsayin aro na kakar wasa daya. Arsenal sun bayyana Neto a matsayin matashin dan wasan gefe da suke so wadda zai maye gurbin Bukayo saka.
Sai dai ana ganin wannan cinikin zai kasance mai wahalar gaske ga kungiyar Arsenal. Sabida Wolves bazasu so rabuwa da dan wasan acikin sauki ba, domin kuwa zasu iya neman kudade masu yawa daga wurin Arsenal, waddda ake ganin hakan zaisa Arsenal su hakura da cinikin. Sai dai kuma ɗan wasan zai iya taka rawar ganin wurin yiwuwar cinikin dan wasan sabida yana da burin zuwa Arsenal.
Arsenal dae sun tuntubi wakilin dan wasan wato Jorge Mendez akan matashin dan wasan dan kasar Portugal. Neto a shirye yake da yazo kungiyar Arsenal sai dai bazai matsawa kungiyar sa ta Wolves akan dole su siyar dashi ba. Zuwa yanzu dae Arsenal basu kaiwa Wolves tayin siyan dan wasan ba.
A daya bangaren kuma Arsenal suna da wasu yan wasan da suke so su siyo idan har basu sami damar daukar Neto ba. Sai dai haryanzu ba'asanar da sunayen yan wasan ba.