Tattaunawa naci gaba da wakana tsakanin OGC Nice da Arsenal akan Nicloas Pepe. Sai dai babu yarjejeniyar siyan dan wasan daga baya ma'ana But Option acikin cinikin. Dan wasan zai tafi OGC Nice zaman aro ne na kakar wasa daya.
Dukkan kungiyoyin biyu sun matsu suga sun kammala wannan cinikayyar. Albashin dan wasan shine abinda yarage kawai a kammala cinikin cinikin.
Source: [Fabrizio Romano]
Liecester City zasu sanar da farashin dan wasan tsakiyar su wato Youri Tielemans domin ganin sun siyar da dan wasan.
Arsenal sune kungiyar da sukafi neman dan wasan sai dai haryanzu basu kai wani tayi ba. Youri Tielemans ya kwantar da hankalinsa domin yasan cewa zai iya komawa kungiyar Arsenal.
Source: [🇧🇪 Nieuwsblad Sport]