Martin Odegard: Eh kwarai dole muci gaba da jajircewa, domin bamuyi komai ba tukuna.
Kakar yadda nagaya muku dole ne mu natsu, dole ne muci gaba da aiki tukuru sannan mu tsaya da karfinmu. Mu maida hankalinmu akan kowana wasa dake gabanmu, mu kuma fuskanci wasar tamkar wasan karshe (Final) wannn shine abinda mukeso muyi. Wannan shine irin burin da muke dashi acikin zukatanmu. Zamu tafi wasa bayan wasa sannan muyi kokarin ganin munyi nasara a kowana wasa. Yanzu dai munfara da kafar dama, musamman idan aka kwatanta da yadda muka fara kakar wasa da ta gabata. Wannan lokacin zamuce ya danfi kyau fiye da kakar wasa ta baya. Muna cikin farin ciki a yanzu sabida munyi nasara a Wasanni uku.
Munci kwallaye masu yawa dan haka muna farin ciki. Dole ne mu natsu mu tsaya da karfinmu sannan muyi aiki tukuru dan ganin munci wasa na gaba.