LABARAN TRANSFER NA ARSENAL

KWANAKI SHIDA SUKA RAGE!!


Yau saura kwanaki shida suka rage a rufe kasuwar musanye yan wasa.

Akwai muhimman abubuwa guda biyar dake gaban Edu da Arteta, yazama kusan dole ne Edu yayi wadannan abubuwan guda biyar acikin kwanaki Shida.

Abu na farko shine....

Dole Edu Yayi duk mai yiwuwa wurin ganin yanemo mafita akan Nicolas Pepe.

Abu na biyu Shine...

Dole Edu Yayi kokarin kawo dan wasan gefe da zarar ya sallami Pepe, domin bazaiyiwu a zauna da Saka a matsayin dan wasan gefe bahago shi daya ba, dole ne a nemo wadda zai maye gurbin Pepe.

Abu na uku.

Dole ne a nemo mafita akan Bellarin acikin kwanaki Shida da suka rage.

Abu na hudu....

Maganar Tielesmans dole ne Edu ya nemo mafita, ko su biya kudin Tielesmans ko kuma su sayi wani dan wasan.

Abu na biyar shine...

Dole ne Edu yasan yadda zaiyi Maitland-Niles yabar kungiyar Arsenal kafin arufe kasuwar musanye yan wasa.

Wadannan sune abubuwa guda biyar da Arsenal zasu maida hankali akansu kafin a rufe kasuwar musanye yan wasa.

Da wannan dalilin nakeji karmuyi tunanin faruwar wani abu acikin wannan satin. Kowa ya jira zuwa ranar monday dan ganin me zai faru.

Domin babban abinda Arsenal suka maida hankali akai yanzu shine ganin sun sallami Pepe yatafi OGC Nice. 

To daga nan ne komai zai fara wakana akan sabon dan wasa da za'a siyo.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post