GABRIEL JESUS YAYI WATA MAGANA MAI BAN MAMAKI

 Gabriel  Jesus: Da farko dai, na yi farin ciki sosai domin mun taka rawar gani sosai ga kungiyar mai matukar  wahalar wasa. Munsan kwarewar tawagar yan wasan  Leicester, domin suna da ’yan wasa masu kyau, musamman Vardy yana daya daga cikin manyan 'yan wasan gaba da na sani a wannan gasar  don haka na yi farin ciki da maki uku da muka samu akansu.

 Gabriel Jesus: Wani lokaci 'yan wasa kowa yana  son ya buga wasa kuma nima haka yake garenni.  Nazo Arsenal ne dan na taka leda. Ni da Eddie Nekthia muna iya cin kwallaye masu kyau - yana da kwarewa sosae  da kuma  kwarin gwiwar yin wasa shima.  Ina ganin Arsenal na da 'yan wasan gaba biyu masu kyau.

 Gabriel  Jesus a kan ko ya kamata ya yi hat-trick?

 Hakika, hakika!  Ina aiki tukuru a kowana rana dan ganin na zura kwallaye a zare. Nayi dan bakin ciki saboda rashin cin kwallaye uku, to  amma ina matukar farin ciki, ba kawai saboda kwallayen da naci ba, sai dan  saboda yadda muka taka leda a wasan.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post