KALAMAN ARTETA AKAN THOMAS PARTEY

Mikel Arteta ya yabawa Thomas Partey a yayin ganawa da yayi da manema labarai a jiya jumma'a gabanin wasan da za su kara da Leicester City a ranar Lahadi.

An yiwa Arteta tambaya ko zamowar Thomas Partey gwarzon dan wasan watan Fabrairu na nuni da irin gudummawar da yake badawa ne a matsayinsa na babban dan wasa ne a Æ™ungiyar? 

 Eh! kuma yana nuna abin da zai iya yi," in ji Arteta.

 Kuma ya kamata ya kasance tare da abokan wasansa wurin taimaka masu saboda iyawar da yake da ita ita ce mafi kyawu a cikin kungiyar.  Yanzu yana bukatar ya nuna akai-akai cewa zai iya yin hakan.

 Taya ka iya daidaita salon wasan Arsenal don dacewa da wasan Partey?

 Arteta yace mun chanza tsarin  salon wasan Arsenal a cikin yan wasanni da suka wuce wurin amfani da salon wasa 4-3-3, maimakon 4-2-3-1 da ya saba dashi tun a farkon wasansa. 

 Munyi hakanne sabida  Granit Xhaka yana taka rawar gani sosai musamman idan yana tare da Partey yana aiki a matsayin dan wasan tsakiya mai zama wadda baya yawan tafiya gaba. Arteta yace munyi wannan chanji ne dan samun abinda muke bukata daga Thomas Partey.

 Arteta yaci gaba da cewa Muna kokarin daidaita salon wasanmu da kadan kadan.

 Wasu daga cikin abubuwan da muke yi shi ne kokarin daidaita salon wasanmu ta yadda zai bashi damar taka leda yadda yakeso batare da fargaba ba. 

Ina ganin yana fahimtar salon wasan sosae.

 Aiki ne da muke yi a filin  atisaye dan Æ™oÆ™arin sanarwa   yan wasanmu damar taka ta yadda suke so gwargwadon iko.

 Arteta ya yi imanin cewa salon da Partey yake nunawa yanzu ya nuna cewa ya fara fahimtar salon wasan Primier League bayan kwashe watanni 20 da zuwan sa Ingila. 

 Dole ne mu gane cewa ya sami raunuka sosae a baya wadda kusan hakan shine sanadiyar rashin ganinsa a ainihin yadda muka sanshi.

 Yana bukatar ya saba da salon tsarin wasan daban-daban fiye da yadda ya saba dashi a baya,  kuma yanzu ina ganin yana cikin kyakkyawan lokaci da zaiyi hakan.


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post