KALAMAN ARTETA AKAN WASAN WATFORD

Arteta: Mun yi wasa mai  kyau sosai. Musamman wurin zuwa gaba kuma mun zira kwallaye uku masu ban sha'awa, amma mun kasa saka kuzari da jajircewa wajen kare kwallayen da muka saka. Idan irin hakan yana faruwa  Kuma a  wajen gida, (Away) za ku sha wahala, domin hakan shine ya bamu wahala a yau.

 Arteta: Na yi matukar farin ciki da muka yi nasara, amma dole muyi gyara  wurin iya  sarrafa wasa  musamman lokacin da muke cin  3-1, dole ne mu dinga taba kwallo cikin gidan abokan  hamayya kuma lokacin da suke kokarin kai mana hari,ban daidai lokacin ya kamata muci gaba da kai masu hari amma ba mu yi hakan ba.

 Arteta akan Saka kwazon da saka yakeyi tun bayan  kammala gasar Euro.

 Ina tsammanin hakan ya kasance sanadiyar   ƙarfafa shi. Domin ya gane a duk lokacin da kake  cikin mawuyacin hali zaka sami goyon baya daga wurin mutane. Yana buƙatar mantawa da abinda ya faru ya maida hankaliinsa akan abin da yake yi.

 Arteta akan tai makawa da yayi wurin cin ƙwallon  Martinelli

 Idan kowa zai iya bada gudunmawa to yayi kyau

 Arteta akan kokari  Saka da Odegaard

 Ina ganin  mun yi kokari wurin shigar da kwallo gaba,  amma bamu nuna kuzari iri  da kuma jajircewa wajen kare hare haren da suke kai mana ba. Idan hakan tana  faruwa zamu sha wahala. Mun bari sun saka mana kwallaye har biyu, munyi sa'ane ma domin sun sami wata damar sake saka kwallo daya zuwa biyu.


 Arteta akan kokarin Lacazatte

 Har yanzu ba zai yi farin ciki ba saboda yana son zura kwallo a raga, abubuwa da dama da yake yi a kungiyar suna da ban mamaki.

 Arteta akan mataki na hudu (Top 4th)

 Ba na son kallon tebur da yawa saboda muna da wasanni a hannu. Za mu yi wasanni daban-daban kuma abu daya da nasani shine  ba zan iya chanza  sakamako ba idan yazo.

 Arteta akan idan akwai yiwuwar Lacazatte yaci gaba da zama a Arsenal!

 "Akwai yiwuwar!  karshen kakar wasa idan muka san inda muke za mu zauna da  'yan wasan uku domin yanke shawara.

 Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post