Arteta ya gana da manema labarai akan wasan Brendford da za'a buga. Ga ƙafan daga cikin abubuwan da Arteta yayi magana akansu.
Ko kayi zama da Shuwagabannin Primier League game da jan kati da aka bawa Gabriel Martinell?
ARTETA: Bamuyi wata magana ba tukuna, amma muna shirin yin hakan nan ba da jimawa ba, amma dae mun riga mun fada fili akan rashin fahimtar bada wannan jan katin.
Wana irin kallo kake wa jan katin tun bayan faruwar lamarin?
Ban san wana irin kallo nake masa ba. Ina da bidiyoyi da yawa da mutane suka aiko mana dashi na tsawon shekaru da suka daban-daban akan al'amari makamancin wannan da kuma yadda yadda akayi hukunci. Na fadi ra'ayi na tun ranar da akayi wasan, babu wani abu da za mu iya yi a yanzu game da shi.
Mezakace akan rashin zura maku kwallo a zare da ba'ayi?
Duk wata ƙungiya da ke son zuwa gasar nahiyar turai (Champions League) Dole ne ku kasance ba'a iya saka muku kwallo acikin zarenku da sauki. yazama sai ansha wahala sosai kafin za'a iya zura kwallo a raga.
Tsarin wasanmu shine kai hare hare wurin cin kwallo sai dae haryanxu muna bukatar mukara inganta kyaun mu a gaba wurin zura kwallo a zare don samun nasara cikin kwanciyar hankali kuma wannan shine abin da muke aiki akai.
kan murmurewa Bernd Leno daga Covid…
Yana lafiya. Ya warke da kyau, ba shi da wata matsala yanzu. Yayi atisaye a wannan makon kuma yana cikin farin. Don haka zai kasance damu a gobe.
Ko kuna cikin kungiyoyin da zasu iya karewa a Top 4th?
Muna nan inda muke. Mun sami damar zama inda muke a yanzu ne sabida kwazon yan wasan mu. Dan haka ina jinjinawa yan wasan da kowa da kowa, musamman magoya bayanmu, domin muna bukatar goyon bayansu. Domin goyon bayansu suna da matukar muhimmanci, muna jindadin yadda suke goyon bayanmu, sun fahimci wajabcin goyon bayan wadannan matasan 'yan wasa.
Wannan shine abin da muke bukata, duk lokacin da muke wasa a gida da kuma lokacin da muke wasa a waje muna jindadin irin goyon bayan su saboda yana kara mana karfi.
Me zakace akan alakar da ke tsakanin magoya bayanku da 'yan wasanku?
Ina jindadin hakan. Muna bukatar hakan ya zama ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan mu a cikin wannan aikin da kuma abin da muke ƙoƙarin cimma.
A baya na taba fadin hakan tun lokacin da magoya baya basu da a ba su izinin shiga filin wasa. Domin yana karawa yan wasa kwazo aduk lokacin da suka ji ihun magoya bayansu acikin filin wasa to kwazonsu yana karuwa ne aboda sun san yakanata su farantawa magoya bayansu rai.
Ko ana ci tarar 'yan wasan ka da ake basu jan kati?
Bana so na yawaita magana akan wannan zancen. Sabida yawan magana akansa zai sanya mu fadi wata magana mai muni.
Ko kana ganin akwai kyama da ake yiwa yan wasaka sabida jan katin da suke samu?
Ba na son in ce wani abu makamancin haka. Na dai san akwai dalilai daban-daban ta yadda muka samu wadannan jan kati, amma ko ta yaya dole ne mu dakatar da shi sabida hakan zaiyi mana illa da kuma sakamakon wasanni mu. Ya zama dole mu mayar da hankali mu wurin gyara hakan domin bazamuyi ta zargin alkalan wasa ba.
Dole ne mu yi imani cewa alkalan wasa za su yi abin da za su yi, kuma dole ne mu yi imani cewa muma za mu yi abin da za mu yi. Shi ke nan.
Thierry Henry ya ce idan har Arsenal basu kare wannan kakar wasan a mataki na hudu ba, to kun kasance acikin marasa nasara. Ya kake ganin kalaman sa?
Ban sani ba, ban karanta abin da ya ce ba. Kowa yana da ’yancin faɗin abin da yake so, hakan yasan kowa yana da damar ya rubuta abinda yakeso. Gobe manufarmu ita ce mu taka leda gwargwadon iyawarmu kuma muyi nasara a wasan, shi ne manufarmu.
Lucky 88 Casino, Tunica Resorts, MS - MapyRO
ReplyDeleteLUCKY 88 CASINO, TUNICA RESORT, Robinsonville MS 38664 - 군산 출장마사지 Use this simple 동해 출장샵 form to 구미 출장안마 find hotels, motels, and other lodging near 순천 출장마사지 Lucky 88 군포 출장샵 Casino,