Rahoton bbc Hausa
Abin da ya kamata ku sani kan wasan Chelsea da Arsenal
Arsenal ta ziyarci Chelsea domin buga wasan mako na 15 a gasar Premier League da za su fafata ranar Lahadi a Stamford Bridge.
Arsenal tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki daya tsakani da Manchester City, wadda ta koma matakin farko.
City ta yi nasara a kan Fulham da ci 2-1 ranar Asabar, dalilin da ya sa kungiyar Etihad ta koma ta daya kenan.
Chelsea kuwa tana ta bakwai mai maki 21, wadda ta yi karawa 12 kawo yanzu.
Wasan da suka kara a bara tsakanin Chelsea da Arsenal:
2021/2022
Premier League Laraba 20 ga watan Afirilun 2022
Chelsea 2 - 4 Arsenal
Premier League Lahadi 22 ga watan Agustan 2021
Arsenal 0 - 2 Chelsea
Wasu batutuwan da ya kamata ku sani kan karawar
Arsenal na fatan doke Chelsea karo na uku a waje a jere, kuma a karon farko tun bayan bajintar hakan a 1974.
Gunners ta ci wasa uku daga hudu da suka fafata a baya a Premier, wadda a baya ta yi nasara a biyu daga haduwa 17, wato canjaras shida aka doke ta tara daga ciki.
Chelsea
Ba a doke Chelsea a wasa 12 a gida ba a dukkan fafatawar da ta yi a bayan nan, rabon da ta yi rashin nasara tun 4-2 a hannun Arsenal ranar 20 ga watan Afirilu, kenan ta ci karawa bakwai da canajaras biyar a Stamford Bridge.
Sai dai wasa daya Chelsea ta ci a karawa 12 da ta yi a gida da kungiyoyin da ke shidan kan teburi a kakar nan.
Wanda ta yi nasarar shi ne 2-0 a kan Tottenham a Janairun 2022.
Watakila Pierre-Emerick Aubameyang ya zama na biyu, bayan Cesc Fabregas da ya ci Arsenal da Chelsea a Premier League a karawa tsakanin kungiyoyin.
Aubameyang ya zura kwallo 68 a wasa 128 da ya yi wa Gunners tsakanin 2018 zuwa 2021.
Raheem Sterling ya ci Arsenal kwallo takwas a Premier League, Bournemouth da Watford sune ya fi zurawa kwallo har tara, sannan Gunners.
Arsenal
Arsenal ta lashe wasa 10 daga 12 da ta buga a kakar nan a Premier.
Kungiyoyi tara daga 10 sun lashe babbar gasar tamaula ta Ingila da suka yi irin wannan bajintar ta Gunners a karawa 12, in banda Newcastle a 1995-96.
Arsenal ta ci wasa biyar daga 50 da ta ziyarci Stamford Bridge da Old Trafford da Anfield da Etihad da kuma Tottenham.
Kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta lashe dukkan karawa hudu ta wasan hamayya ta birnin Landan a kakar nan.
A kakar 2021/22 Gunners ta ci wasa biyar daga 10 a karawar hamayya ta birnin Landan da cin daya da rashin nasara hudu.
Gabriel Jesus bai ci kwallo ba a wasa takwas a lik da kofi, wanda rabon da ya zura kwallo a raga tun wasan Tottenham da Gunners ta ci 3-1 ranar 1 ga watan Oktoba.
Source BBC HAUSA