LABARAN WASANNIN ARSENAL 27/10/2020!!

      MUSTAFI NASON BARIN ARSENAL

mai tsaron bayan Arsenal dan kasar Germany wato Shokdran Mustafi nason barin yanuna sha'awarsa nason barin kungiyar ta Arsenal.

Arsenal sunyiwa dan wasan tayin karin kwantaragi amma dan wasan yayi watsi da tayin na Arsenal.

Arsenal dai sun siyo Mustafi ne daga kungiyar kwallon kafa ta Valencia a shekarar 2017.

Tabbas mustafi yayi kokari a Valencia amma ayazu banga amfanin mustafi a Arsenal ba. Taya dan wasan da idan har yayi wasa 5 to sai yayi kuskure da zata janyo aci mutane amma shi arsenal suke kokarin kara masa Contract? 

Wannan wani son zuciya ne kawai.
Ni nakasa ganewa cikin Arsenal da Mustafi wa yafi hauka?
Arsenal da suka masa tayin wani Contract?
Ko mustafi da yayi watsi da tayin?

Me Arteta yagani awurin Mustafi?
Mustafi yana ganin idan yabar Arsenal zai iya zuwa Babban kungyar da tafi Arsenal ne ko yagaji da kungiyar ne?

 Mustafi bai yi wani abun azo agani ba a kungiyar Arsenal.

Amma duk da haka arteta yana son Mustafi cikin yan wasan da Arteta yake son amfani dashi a matsayin dan wasan baya.

Kushiga nan👇👇

   OZIL SHI KEDA LAIFI AKAN RIKICINSHI DA ARTETA!!

Tsohon dan wasan bayan Arsenal dan kasar Cameeron wato Laurent yace Ozil ke da laifi akan rashin sanya sunansa da Arteta yayi a tawagar da zasu bugawa kungiyar Arsenal gasar Primier league da Europa na zangon farko.

Lauren wadda yana cikin tawagar yan wasan Arsenal da sukayi Unbetean a shekarar 2003-2004 yace duk wani wadda yake bibiyar Arsenal kuma yana sonta to zaiso ace babban dan wasa kamar Ozil yana kungiyar.  Lauren yace rashin Ozil a kungiyar ba karamin abin bakin ciki bane.


Sai dai dan wasan yace hakan laifin Ozil ne. Domin kuwa kafin Arteta yazo makamanci haka yafaru tsakanin Ozil da Unai Emery yanzu kuma gashi yana faruwa da Arteta. Wannan matsalar zamu iyq cewa ta Ozil tafi yawa akan masu horawar (Coaches)  ko kuma kungiyar (Management).

Tabbas wannan abin yayi matukar taba Ozil a zuciyarsa nima (Lauren) ya tabani sosae a zuciyata. Domin zanso naga babban dan kwallo irin Ozil yana wasa a kungiyar da nakeso.

Kudanna nan 👇👇


Arsenal itace kungiyar da nake bibiya,  itace kungiyar da nakeso dole zanso naga babban dan wasa yana taka leda a kungiyar.

Lauren yace dole akwai wasu boyayyun abubuwa da bamu sani ba akan wannan al'amari na Ozil.


   OZIL YATAIMAKAWA YARA YAN MAKARANTA


Mesut Ozil ya aikawa makarantar whitings Hilss da abinci acikin kananan robobi dan rabawa kanana yara yan wannan makarantar. Kananan yaran su 70 ne suka sami wannan abincin.

Kushiga kugani👇👇


Ozil Allah yasakama da mafificin Alkhairi. Allah yabiya ma bukatunka. Allah kuma yakawoma mafita cikin wannan jarabawar da kashiga. Ameen.


    AUBAMEYANG YAFARA KOYON KALMOMIN LARABCI!!


Dan wasan gaban Arsenal dan kasar Gabon wato Pierre Emerick Aubameyang yace yana son Mohammed Elneny sabida Elneny yakasance kamar shi mai yawan murmushi kuma a kullum yana cikin farin ciki.  

#Aubameyang yace Elneny dan wasa ne mai hazaka sosae wadda duk lokacin da ya shigo wasa kokarinsa yakawo wa yan gaba kwallo.

Kushiga cikin nan 👇👇

#Aubmeyang yace yanzu haka sunfara shakuwa da Mohammed Elneny wadda hartakai ga yafara koyon wasu kalmomin larabci daga wurin Elneny din.

#Aubameyang yace yanzu haka yasan ma'nar #Alhamdulillah!  da kuma #Habibi!



                        MIKE DEAN

Mike Dean shine alkalin wasan (Refree) da zai alkalanci wasan Arsenal da  manchester United wadda za'abuga ranar Asabar mai zuwa.

Ko ya kuke ganin adalcin wannan alkalin wasan musamman alokacin da zai alkalanci wasan manchester United??


ALEXENDRE HLEB YACE YAYI KUSKURE!!


Tsohon dan wasan Arsenal dan kasar Belarus wato Alexendre Hleb yace yayi da yasanin barin kungiyar Arsenal.


Dan wasan wadda yabar Arsenal a shekarar 2008 zuwa Bacerlona yace baisan meyasa yabar Arsenal a 2008 ba kasancewar lokacin yana cikin farin ciki a kungiyar amma haka yabar Arsenal yakoma Bacerlona.

Hleb yace a wanan shekarar Bacerlona babbar kungiyace d tafi kowata kungiya haskakawa a duniya. Amma a wannan lokacin ina cikin jindadi a Arsenal.

#Hleb ya bayyana barinsa Arsenal amatsayin wani kuskure da yayi a harkan kwallon kafa.

   GABRIEL YA BAWA MAGOYA BAYAN ARSENAL HAKURI!!

Sabon dan wasan bayan Arsenal dan kasar Brazil wato Gabriel Mangalheas yace haka wasa take wani lokaci zakuyi iya kokarnku wurin ganin kunyi nasara amma sai hakan taki samuwa.

#Gabriel yace zasuyi iya kokarinsu wurin ganin sunyi nasara a wasa na gaba.

Dan wasan yayi wannan maganarne a shafinsa na Twitter.



Kuci gaba da kasacewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.




Admin
Prince Tije.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post