SHIGA KA KARANTA HIRAR DA AKAYI DA MIKEL ARTETA JIYA!!

  CIKAKKEN HIRAN DA AKAYI DA ARTETA!


A jiya Laraba ne akayi hira da kocin Arsenal wato mikel Arteta akan wasu muhimman abubuwa!

Antanbayi kocin Arsenal din abubuwa da yawa wadda suka hada da..

Mezakace akan wasan liecester city?


Arteta: Eh! Yan wasa na sunyi kokari matuka musamman a zangon farko (First Haf) munkai hare hare sosae wadda ya kamata ace munsha kwallo amma hakan baiyiwu ba. Bamuyi wani kuskure sosae a zargon farko ba, kuma bamu basu wata dama ba. Kuna ganin har kwallo muka jefa cikin raga amma aka kashe mana kwallon. Amma kuskure daya mukayi nabasu dama da barin dan wasansu batare da wani ajikinsa ba suka zura mana kwallo a ragarmu. Wannan babban abin bakin ciki ne rashin nasara a irin wannan wasa da bakasha wuya ba amma karasa wasar.


Kushiga nan 👇👇

Mezakace akan rashin shan kwallo (Scoring) na Lacazette da Aubameyang?

Arteta: Na damu matuka sabida bamu iya cin kwallo musaman alokacin da muke wasa a gida. Wannan abin damuwa ne kwarai da gaske. Dama daya tak muka samu a zango na biyu (Second Half) a wasanmu da Liecester City itace ta Bellarin. Sam liecester City basu sami wata dama ba a wasan sai a minti na 75-80 da fara wasan amma sunyi amfani da wannan damar sun ci kwallo. Wannan abin bakin ciki ne,  zamuyi gyara wurin bawa yan gabanmu damar kai hara sosae tare da shigar da kwallo gidan abokan gabanmu. Muna gyara akan hakan kuma muna fatan zamu yi nasara aka wannan gyaran da mukeyi.

Mezakace akan raunin da David Luiz yasamu?

Kushiga kusha kall👇👇

Arteta:  Luiz yasami dan karamin matsala ne a cinyarsa. Bazai buga wasan Europa League na gobe alhamis ba. Haryanzu likitoci suna duba lafiyarsa.


Ko kana farin ciki da dawowar  shokdran mustafi daga raunin da yasamu?

Arteta:  kwarai ina farin ciki sosae sabida tun bayan da nafara aiki a wannan kungiyar yayi matukar kokari. Sai dai yayi dogon jinya yakuma yi aiki tukuru dan ganin yasami lafiya haryadawo wannan matsayi da yake ayanzu. Ina fatan zaici gaba da kokari kamar yadda nake da yarda akansa. Kuma zanci gaba da bashi wasa dan ganin ya haskaka kamar yadda yayi abaya kafin yasami rauni.

  Mezakce akan kwarin guiwar(Confidence) na mustafi?

Arteta: Eh akwai yar karamar matsala da yake dashi na rashin kwarin guiwa (Confidence) aduk sanda yake da kwallo a kafarsa. Amma zamuyi kokari muga munsanya masa kwarin guiwa. Ya rage nashi shikuma sai yanuna  kokarinsa akan hakan.


Ya yanayin damuwarka akan rashin nasara da kakeyi kwana biyu?


Arteta:  Kwarai nadamu matuka sabida wannan kungiyar tana da bukatar nasara akan duk wani wasanninta. Munyi rashin nasara a hannun manchester City da Liecester City duka daci 1-0.  Kunga yadda mukayi iya kokarinmu  a wannan wasa amma munyi rashin nasara sakamakon wasu kananun kuskure da mukayi. Magoya bayanmu sunyi tsammanin wani abu daga garemu a wadannan wasan. Zamuyi kokari muyi gyara akan hakan.
Ya yanayin damuwarka akan rashin zura kwallo da kuma gudun mawar nkethia?


Kushiga ku karanta👇👇

Arteta: Bashi kadai zaibamu gudunmawa ba. Muna bukatar gudunmawar kowa. Ni aikina shine na samo masu mafita tare da basu yanayin yadda zasu dinga kai hara mai kyau. Idan kun lura a wasanmu da Liecester sun rufe gidansu sosae amma duk da haka sai da muka shigesu kusan sau biyar zuwa shida acikin minti 45. Ya kamata ace munjefa masu kwallo acikin raga amma hakan baisamu ba. Bamu saba da irin kalar wasan da liecester suka buga mana  ba. Sabida bamu hadu da wata kungiya mai kalar wannan wasan ba. Amma abinda nafahimta shine liecester sun girmamu kuma sun tsorata damu matuka ta yadda sukazo gidanmu suka kasa fitowa su buga kwallon da suka sabayi. Yazama dole mu dauki hakan da muhimmanci agaremu,  kuma wata damace agaremu domin idan sauran kungiyoyi zasu fara tsoronmu haka hartakai ga suna kasa fitowa suyi wasa damu to ina mai tabbatarmuku zamuyi nasara a wasanni masu yawa.

Kudanna  nan 👇👇

Mezakace akan kokarin da kungiyoyi primier league keyi?


Arteta: Tabbas acikin watanni 8 zuwa 10 ansami ci gaba sosae a gasar primier league. Ko wata kungiya tayi karfi matuka. Wannan abune da nadade banganshi ba a gasar primier league. Yanzu abune mai wuyar gaske kayi nasara cikin sauki a gasar primier league. Ina tunanin yanxu gasar yana mataki da yadace.
Mezakace akan goyon bayan da Ozil kenunawa a shafin twitter a duk lokaci da Arsenal ke wasa?

Arteta: Bancika damuwa da harkan yanar gizo ayanzu ba. Amma dama ina tsammanin haka daga duk wani wadda yake Arsenal. Ina jinjina masa.


Mezakace akan Dundalk?  Kanaga zasu iya kokari?


Arteta: Acikin ma'aikanmu akwai yan Ireland kasar da kungiyar take kenan. Kungiyace da take da abinda za'adamu aduk lokacin da za'ayi wasa dasu. Daga yadda naga kungiyar suna da babban mai horawa wadda yake da natsuwa tare da karanta yadda wasa ke tafiya. Kuma akwai kyak'kyawar fahimta tskanin sa da yan wasansa. Aduk lokacin da suke wasa zakaga yadda suke da hadin kai da yadda suke fahimtar juna ayayin wasa, zasu matukar bamu wahala dan zasuxo gidanmu ne da karfi sosae na nuna kwarewarsu. Zasu zo gidanmu da karfi sosae na son ganin sunyi nasara musamman yadda suke ganin baizamo dole suyi nasara agidanmu ba. Ina tsammanin zasu sanya dukkan karfisu awannan wasa na son ganin sunyi nasara akanmu.

Kubude nan 👇👇

             Ko Willian zaiyi wasa gobe?

Arteta:  Willian yayi kwana biyu yana atisaye damu dan haka zai iya buga wasan na gobe.

            Ko Saka zai iya buga wasan?


Arteta: Yasami yar karamar matsala ne na dukan da aka masa a cinyarsa. Amma yayi atisaye damu babu wata damuwa.


Ko wasan da zaka buga da manchester United zaisa kaki fitowa da manyan yan wasanka a wasanka da Dundalk?


Arteta:  Eh zamuyi kokari a kowana wasa musaka yan wasan da yakamata. Amma gaskiya a yan kwanakin nan munsami matsala na rauni da yan bayanmu suka samu.  Dole mu maida hankali da tunanin yadda zamuyi amfani da yan wasan bayanmu domin idan muka sake rasa guda daya ackin wadda suke da lafiya yanzu to tabbas zamu shiga cikin babban matsala. Dan haka dole mu lura da yadda zamu dinga amfani da yan wasa acikin wasanninmu biyu zuwa uku.

Kushiga kugani 👇👇

Ko Nelson zai sami buga wasanni sosae a wannan kakar wasan?


Arteta: Gaskiya munso mutura Nelson aro (Loan) a wata kungiyar da zaisami buga wasanni sosae. Sabida muna da yan wasa da suke buga wurinsa (Position) nashi sosae. Amma yanzu haka yana matukar kokari afilin atisaye. Dan ganin yasami damar buga wasa. Abinda ke burgeni dashi shine yadda yake cikin farin ciki da nuna rashin damuwa duk da baya buga wasa a kungiyar. Amma zanbashi dama alokacin da yadace. Kuma abubuwa zasu iya chanxawa musaman yadda muke samun masu rauni da kuma yadda muke da wasanni sosae agabanmu. Dan haka zaisamu dama. Yadai rage nashi duk lokacin da yasami dama ko yayi amfani da ita ko yaki amfani da'ita.



Amma me yahana kutura Nelson aro (Loan)?

Kudannan nan 👇👇

Arteta:  Wasu abubuwane suka hana mu turashi loan. Shi dai  Nelson bayason barin  Arsenal yanuna yason yazauna dan yayi kokari da zaisa yasami wurinsa. Tunda muka fahimci haka sai muka kyaleshi duk da nasan samun damar buga wasa yadda yakeso abune mai wahala wadda hakan zaijanyo bazaisami ci gaba a wasansa ba. Amma abubuwa suna iya chanxawa cikin dan karamin lokaci idan yayi wasa yadda nakeso me zaihana mubash wasa? Babu.





Wannan shine abinda Arteta yace  a hirar da akayi dashi jiya.


Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal cikin harshen hausa.


Admin
Prince Tije.


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post