KAYATAT'TUN LABARAN ARSENAL!

 WILLIAN YACE BAI TABA AIKI DA WANI MAI HORASWA IRIN MKEL ARTETA BA!


Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Brazil wato Willian yace bai taba aiki da wani koci irin Arteta ba. Dan wasan wadda Arsenal ta dauko daga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea yace wurin (Possition) da yake bugawa  a kugiyar yanzu  wani sabon abune agareshi a harkan kwallon kafa. Domin ina tsayuwa na dade batare da kwallo tazo wurina ba. Hakan yasa nakanyi kokarin chanza wuri (Possition) amma duk lokaci da nayi kokarin hakan sai Arteta yace natsaya awurin kwallon zatazo wurina. Duk da kasancewar bana yawan yawo acikin fili hakan baya nufi banajin dadin wasa. Ina koyon sabbin abubuwa daga wurin Arteta.
Kushiga nan👇👇
Dan wasan ya bayyana hakanne ayayin wata hira da yayi da wata gidan jarida dake kasar Brazil.

Sai dai bayan wannan batu da dan wasan yayi wasu  jaridu na kasar England sun fassara hakan amatayin Willian yanuna bayajin dadin,  wurin (Possition) da Arteta yake sakashi ne.

Dan wasan yafito ya karyata wadannan jaridun kasar England din inda yace shi bahaka yake nufi ba. Kuma yana kira ga yan jaridun kasar England da sunemo kwarar'run masu fassara masu labarai. Willian yafadi hakanne sabida yayi hirar ne da yaren kasar'sa ta Brazil.


ARTETA YAYI DA YASANIN RASHIN YIWA SALIBA RIJISTA A GASAR EUROPA!

Kocin Arsenal wato mikel Arteta yace yayi bakin ciki na rashin yiwa Saliba rijista a gasar  Europa League.

Matashin dan wasan wadda Arsenal ta siyo a bara daga kungiyar kwallon kafa ta Saint Entienne akan kudi €27m. Bai samu shga cikin jerin wadanda zasu wakilci kungiyar Arsenal a gasar Europa league a wasannin rukuni ba (Group Stage) sakamakon anso abada aron (Loan) din dan wasan zuwa wata kungiya.
Kudanna nan 👇👇
Arteta yace bamu saka sunan dan wasan bane sabida muna da yan baya masu yawa kamar irinsu David Luiz,  Gabriel Mangalheas,  Rob Holding,  Shokdran Mustafi. Nayi tunanin Pablo Mari zai dawo daukar horo acikin makonni biyu sai dai ansami tsaiko akan hakan wadda yanzu munrasa Mari da Saliba duk da kasancewar Saliba'n yana da lafiya. Wannan hukunci nawa baiyimin dadi ba.

Arteta yace yanzu haka abunda ake bukata akan Saliba yafara samuwa domin kuwa ayanzu dan wasan yafara jin turanci,  sannan yafara fahimatar salon wasan Arsenal.


THOMAS PARTEY YACE ARSENAL WURI NE DA YADACE DASHI!


Sabon dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Ghana wadda Arsenal tasiyo daga kungiyar Ath Madrid akan kudi €45m yace yanzu yana kungiyace (Arsenal) wadda yake kokarin fara gina sabuwar rayuwa aciki wadda zai fara yiwa wasa. Kungiyace da keda komai, wadda suka hada da koci mai basira tare da yan wasa masu kyau. Sannan suna da dabi'u masu kyau.
Shiga kasha kallo👇👇
Partey yace yanayin salon wasan kungiyar abune da ya matukar burgeshi wadda hakan yasa yakejin Arsenal wurine da yadace dashi.


HUSS FAHMY YABAR KUNGIYAR ARSENAL!!

Daya daga cikin manyan ma'aikan Arsenal wato Huss Fahmy yabar kungiyar Arsenal a jiya Jumma'a bayan da ya aikawa kungiar da takardan ajiye aikin nashi (Letter of Resignation) a akwatin sakon kungiyar (Email) Huss Fahmy wadda yazo Arsenal a shekarar 2017 a matsayin mai tat'taunawa akan al'muran da suka shafi kwantaragi (Chief Negotiations).
Click here 👇👇
Huss Fahmy ya taimakawa Arsenal wurin kulla yarjejeniya da  Mohammed Elneny, Nicolas Pepe,  da sabunta kwanaragi Aubameyang wadda yayi acikin yan kwanakin nan,  tare da wasu daga cikin matasan yan wasan kungiyar wadanda suke wasa a under 23, kasa da hakan. Haka zalika Huss Fahmy yataimakawa Arsenal wurin dauko tsohon kocin kungiyar wato Unai Emery da kuma kocin kungiyar na yanzu wato mikel Arteta.

Arsenal dai zasu duba wadda zai maye gurbin Huss Fahmy sai dai kungiyar sunce bazasu bawa wadda zai maye gurbin nasa cikakken Iko ba.

Arteta,  Edu,  da matersacker zasu dauki wani bangare daga cikin harkan kasuwancin kungiyar.

MIKEL ESSIEN YACE PARTEY CIKAKEN DAN TSAKIYA NE!

Tsohon dan wasan tsakiyar Chelsea dan kasar Ghana wato Mikel Essien yace Arsenal sunyi sayay'ya mai kyau na kawo dan wasan kasarsa ta ghana gasar Primier League wato Thomas Partey.
Zaka iya danna nan 👇👇
Partey dan wasan tsakiyane wadda yake iya buga nomba 6. (Central Defender) wadda yafini iya buga wannan wurin (Possition). Inji Essien Yana da natsuwa duk lokcin da kwallo tazo kafarsa. Sannan yana iya daukar kwallo duk lokacin da suka jera da wani dan wasa. Ya na karantar wurin da yake da matsala ayayin  wasa dan taimakaw.
Cikakken dan wasan tsakiya ne.
Essien ya bayyana hakanne ayayin zantawarsa da jaridar Goal.



Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harsen hausa.


Naku
Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post