ABUBUWAN DA TSOFFIN YAN WASA KE FADA AKAN ARSENAL!!

ROY KEANE YACE YANAJIN KAMAR ACE PARTEY DAN WASAN MANCHESTER UNITED NE.

Tsohon dan wasan manchester united dan kasar Ireland wato Roy Keane yace da yaga yadda Thomas Partey yataka leda a ranar  Lahadi a wasan da Arsenal ta doke manchester united daci 1-0 sai yaji inama ace Thomas Partey a Manchester United yake.

Roy keane ya bayyana Partey a matsayin dan wasan tsakiya mai hazaka sosae.

Da naga yadda partey yake wasa sai natuna da tsohon dan wasan Arsenal wato Patrick Viera domin salon wasan Thomas Partey irin na Viera ne.

Kushiga nan

POECHETINO YACE GABRIEL DAN WASA NE DA KOWANA MAI HORASWA ZAISO SAMUNSA A KUNGIYARSA.

Tsohon kocin Totteham dan kasar Argentina wato Moricio Poechetino yace Gabriel Mangalheas dan wasa ne da yake da matukar basira da natsuwa. Duk wani koci zaiyi fatan samun irin wannana mai tsaron bayan a kungiyarsa.

Poechetino ya bayyana hakanne bayan da kungiyar Arsenal ta lal'lasa manchester united daci 1-0 a ranar Lahadi.

RIO FERDINAND NATABA CEWA MAN UNITED SU SAI PARTEY!!

Tsohon dan wasan bayan Manchester United dan kasar England wato Rio Ferdinand yace a watan biyu na wannan shekarar  damuke ciki anyi min tambaya akan wana dan wasa yadace manchester United ta siya? Sai na bada amsa da Thomas Partey. Naso manchester United su sai partey domin dan wasa nane mai matukar kyau wadda zai iya taimakawa duk kungiyar dayake ma wasa.

Kutaba nan 👇👇
GARY NEVILLE YA YABAWA MASU TSARON BAYAN ARSENAL!


Tsohon dan wasan man chester United dan kasar England wato Gary Neville yace yan wasan bayan Arsenal suna kokari sosae wurin tare da kuma zuwa gaba wato attacking. 

Neville yace yan baya gudu 3 da Arsenal suke sakawa suna kokari matuka musaman sabon dan wasansu wato Gabriel mangalheas idan har suka dore ahaka to tabbas baza'asha su kwallaye sosae ba.

PAUL MERSON YACE THOMAS PARTEY SHINE SIYAYYA DA YAFI KYAU A ENGLAND.

Kushiga nan 👇👇

Tsohon dan wasan Arsenal wato Paul Merson ya bayyana Thomas Partey amatsayin dan wasan da yafi kyau acikin duk siyayyan da kungiyoyi gasar Primier league sukayi a wannan kakar wasan.

Paul merson yace idan za'atanbayeshi wana dan wasane yafi kyau acikin yan wasan da kungyoyi Primier leageu suka siyo a wannan kakar wasan? Batare da bata lokaci ba zance Thomas Partey ne. Duba da yadda yake wasa babu wani dan wasa da aka siyoshi a wannan kakar da yanuna zai yi ball kamar yadda Thomas Yanuna.dan haka awurina partey shine siyayyan da yafi kyau a England.


ROY KEANE YACE MAN UNITED SUNA BUKATAR ARTETA A MATSAYIN MAI HORASWA!


Roy keane yace manchester United suna da bukatar mikel Arteta  matsayin kocin kungiyar. Tsohon dan wasan na manchester United ya bayyana hakanne a yayin wata hira da yayi agidan Tv na Sky Sport.  Acikin hirar antanbayi Roy Keane ko menene manchester United ke bukata ayanzu dan ganin sudawo ganiyarsu?

Sai tsohon dan wasan na Manchster United yace suna bukatar wani mai horaswa irin mikel Artate sabida ya kasance mutum mai sa'a.


KOCIN HERTHA BARLIN YA JINJINAWA MATTEO GUENDOUZI.



Kocin kungiyar kwallon kafa ta Hertha Berlin wato Bruno Labbadia ya yabawa Matteo Guendouzi bayan da dan wasan ya buga minti 35 a wasan da kungiyar suka buga da Wolfsburg a ranar Lahadi.

Bruno Labbadia  yace Guendouzi dan wasa ne da yake da basira sosai. Zai taimaka mana matuka domin yana karantar yadda wasa ke tafiya.



Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.


Naku
Admin
Prince Tije.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post