SHIGA KA KARANTA CIKAK'KEN HIRAR DA AKAYI DA ARTETA A JIYA LARABA 4/11/2020

ARTETA YAYI HIRA DA YAN JARIDU A YAU LARABA INDA YA AMSA TAMBAYOYI MASU YAWA.


Dafarko dai kocin Arsenal din wato mikel Arteta yafara ne da bayani akan yan wasan kungiyar ta Arsenal wadda suke fama da rauni.


     DAVID LUIZ YA DAWO DAUKAR HORO.

Dan wasan bayan Arsenal dan kasar Brazil wato David Luiz ya murmure daga raunin da yasamu a wasan da Arsenal ta buga da Liecester City a gasar Primier league. Kocin Arsenal mikel Arteta ya tabbatar da hakan inda yace dan wasan yadawo daukar horo (Training) kuma ashirye yake da ya buga wasan gobe.
Kushiga nan 👇👇
CULLUM CHAMBERS YAFARA ATISAYE.


Dan wasan bayan Arsenal dan kasar England wato Cullum Chambers yadawo daukar horo (Training)  Chambers wadda yasami rauni tun a wasan da Arsenal ta buga da kungiyar Chelsea a 29/12/2029 ya warke abinda yarage masa kawai shine yasami karfin buga wasa.


PABLO MARI ZAI FARA CIKKEN DAUKAR HORO NAN DA YAN WANI LOKACI.

Dan wasan bayan Arsenal dan kasar Spain wato Pablo mari zai dawo daukar horo (Training) nan da sati biyu. Dan wasan wadda yasami rauni a wasan da Arsenal ta buga da manchester City yafara zai fara atisaye tare da abokan wasansa bayan andawo daga buga wasan kasa-kasa (Inernational Duties).

SAI KARSHEN SHEKARA MARTINELLI ZAI DAWO BUGA WASA.

Dan wasan gaban Arsenal dan kasar Brazil wato Gabriel martinelli wadda yake fama da rauni a kafarsa na tsawon watanni 7 yafara gudu shi kadai da kuma yan kanana wasu atisaye da abokan wasansa. Ana saran dan wasan zai fara cikak'ken daukar horo (Training) a karshen wannan shekarar.


Wannan shine bayanin da Arteta yayi game da yan wasan kungiyar  da ke fama da rauni.
Kushiga nan 👇👇

KO ZAKA FARA WASA DA LACAZETTE GOBE?

Zan iya farawa da kowa daga cikinsu musamman yadda naga sukayi Atisaye. Amma sai zuwa goben zanga abinda zai faru.

            MEZAKACE AKAN ELNEY?

Ina tunanin ayanzu yanuna mana alamun zai'iya bayan kalubale da ya fuskanta daga garemu. Tunda tadawo daga zaman aro (Loan) yanuna gudunmawar da zai iya bayarwa acikin kungiyar,  nasan yanzu kowa yaga irin gudunmawar da zai'iya badawa. Ina matukar farin ciki da kokarin da yakeyi.

Kushiga kugani 👇👇

KO HAKAN ZAISA KUKA RA MASA KWANTARAGI??

Zamu dauki komai daki daki amma ayanzu ina matukar jindadin kokarin da yakeyi,  kuma ina fatan zai dore ahakan har zuwa karshen wannan kakar wasan. Ina da tabbacin zamuyi amfani da yan wasa da suka dace


KO YANZU KANA DA TAWAGA BIYU WADDA ZASU BUGAMA PRIMIER LEAGUE DA WADDA ZASU BUGA MA EUROPA LEAGUE?

Eh! Gaskiya bahaka bane kuma gobe zakuga wasu chanje chanje. Nayarda yana da kyau mubawa wasu yan wasa hutu sakamakon wasanni da muke dasu. Sannan akwai wasan kasa-kasa (International Duties) wadda wasu daga cikin yan wasanmu zasu buga wasanni 3. Daga nan har zuwa watan 3 zamuyi wasa a duk bayan kwana 4. Dan haka dole muyi tunanin  da wannan lokaci da kuma tsakiyar kakar wasa sabida zai zama mai matukar wahala.


MEZAKACE AKAN YABONKA DA TONNY ADAMS YAYI?

Hakika dole musami kwarin guiwa daga tsoffin yan wasan wannan kungiyar a duk lokacin da sukace wani abu akanmu da kuma bamu shawara akan abinda suka fahimta da wadda suke ganin idan anyi zaikawo ci gaba a kungiyar tamu. Ina godiya ga goyon bayansu garemu,  hakika nayaba da yadda  naga suke nuna jindadinsu akan yadda muke tafiyar da aikimu. Sannan nasan yadda aikin zaiyi wahala wurin ganin mun maido da martaban wannan kungiya kamar yadda take alokacin d suke wasa. Wannan shine kakubale da yake a gabanmu yanzu.

YAYA GIRMAN KWARIN GUIWA DA KASAMU BAYAN DA KA DOKE MACHESTER UNITED?

Kudanna nan👇👇👇


Kwarai! Hakika wannan shine abinda muke bukata musamman bayan sakamakon wasanmu da Liecester City sabida yadda wasan ya kasance. Amma yadda naga yan wasa na suka fara wasan da kwarin guiwa  a filin wasan  duk da kasancewar bamuyin nasara a wannan filin wasan na Old Trafford. Sannan da kwarin guiwar maganar da nayi kafin wasan da bayan wasan. Bayan wasan nagaya masu haka nakeso mu buga kowana wasa da kwarin guiwa.


WANA IRIN SHIRI KUKEYIWA KOFUNAN DA KUKE BUGAWA A WANNAN KAKAR WASAN?

Wannan tambayace wadda amsart zaiyi wahalar badawa. Ina tunani ayanzu muna isas'sun yan'wasa wadda zamu iya canxawa a kowana wasa.  Muna da yan wasa masu kyau da zamuyi kokari muga munyi kokari aduk wani gasa damuke ciki. Muna buga wasa duk bayan kwana hudu (4) zamu iya samun matsalar rauni,  ko dakatarwa (Red Card) duk wadda yaxo daga ciki zamuyi kokari muga munshawo kan matsalar. Zamuyi iya kokarin mu aduk wani gasa damuke ciki daga nan zuwa karshen wannan kakar wasan.


MEZAKACE AKAN KARFIN MODEL DA RASHIN KARFINSU?

Karfinsu shine yanayin yadda suke wasa amastsayin kungiya daya (Team Work) suna da matukar kyau,  sannan suna da karfi. Zan'iya cewa suna da matukar kyau wurin tare (Defensive) zasu bada wahala wurin fasasu a shigesu. Sannan suna da yan'wasa masu hatsari wadanda  suka iya passing (Bada kwallo asha) Ayanzu teburin a rikice yake sabida daga mu harsu kowa sunci wasanninsu biyu hakan yasa nake ganin wannan zaizama wasa mai wahala agaremu akan wasannin da muka buga a wannan gasar (Europa).

TO KO HAKAN YANA NUFIN ARSENAL DA MODEL SUNE WADDA ZASU TSALLAKA ZUWA ZAGAYE NA GABA?


Bansani ba! Domin illa wasanni biyu aka buga acikin wannan gasa  abubuwa zasu iya cyanxawa a sauran wasannin. Gobe muna gida ne,  dan haka muna da damar zama ta daya akan teburin  munason mukare gasar rukuni (Group Stage) a wannan gasar a matayin ta daya a teburin group namu. Dan munaso muyi saurin samun gurbin shiga zagaye na gaba. Hakan bazaiyiwu mana ba harsai mun doke Model gobe.

MEZAKACE AKAN NASARAR DA MODEL TAYI A WASANNINTA BIYU?

Sunyi kokari sunci wasanninsu biyu batare da sunsha wahala ba. Nasan zasu fito da karfinsu gobe dan haka nake tsammani wasan bazaizo mana da sauki ba gobe.
 Dan haka dole muyi masu shiri sosae dan wasan bazaizo mana da sauki ba.

WASANKA DA MODEL ZAI KASANCE BABBAN WASA KENAN?

Nagaya muku ai suna da yan wasa da suka iya bada kwallo a sha. Basu da tsoro suna da kyau sosae salon wasansu yana da kyau musamman lokacin da suka shigo gidan (Boxes) abokan wasa idan harmuka kalesu suna shigo da kwallo cikin gidanmu (Boxes) zasu iya bamu damuwa.

WANA SAKO ZAKA BAWA MAGOYA BAYAN ARSENAL AKAN SAKE SAKA DOKAR ZAMAN GIDA (LUCK DOWN) KASHI NA BIYU DA AKA SAKA A ENGAND?

Sako na agaresu shine nayi kewarsu matuka da abinda mukeso mugina. Bamu samkasancewa kasancewa dasu ba. Yanzu dole sukoma gidajensu dan su zauna. Inajin wannan wani karin nauyine akanmu nabasu farin ciki da yakamata awannan lokaci mai wahalar gaske nazama agida. Dolenmu ne muyi iya kokarinmu wurin samar masu da farin ciki da  yadace dasu. Sakona garesu shine zamuyi iya kokarinmu wurin  faranta ransu.


WANA SAKO ZAKA BAWA WILLOCK NARASHIN SASHI A GASAR PRIMIER LEAGUE?

Ina dubawa Willilock mafitane wadda tafi dacewa dashi. Amma dan wasane da nake matukar sonshi. Yana da wani kwarewa wadda babu mai irinta a kungiyar,  wadda zamuyi amfani da wannan basira tashi. Kuga yadda yayi kokari a satin da  yagabata yanuna yadda yake da kyau. Dalilin da yasa baya buga wasa kuma shine muna da yan wasa masu yawa a wurin da yake  bugawa.

BAYANAI NA NUNA WILLIAN SALIBA BA YAJIN DADIN HALIN DA YAKE CIKI A YANZU?


Nima banji dadin abinda yafaru ba, kunga yadda nayi kokari samo masa mafita a karshen rufe kasuwar musanye yan wasa. Nayi bayani  yana da bukatar yaje wani wuri wadda zai sami isas'shen wasa amma hakan baiyiwu ba. Yana bukatar yaje wata kungiyar dan muna da masu tsaon baya sosae hakan yasa bamu saka sunansa acikin tawagar yan wasanmu ba wadda hakan abin bakin ciki ne. Bayan nan munsami masu rauni sosae wadda yakamata muyi amfani dashi amma babu hali.

TO KO ZAKU BADA ARONSA (LOAN) A JANUARY?


Gaskiya bansani ba ayanzu munyi kokari mubada aronsa kafin arufe kasuwar musanye yan wasa,  munnnemi kungiya da tadace dashi harmunsamu amma komawarsa baiyiwu ba,  zamu sake  duba yiwuwar hakan nan da wasu makonni,  sannan zamu zauna dashi muga abinda yafi dacewa. Ya danganta ga yadda dan wasan yake sone.



Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal cikin harshen hausa.

Naku
Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post