SHIGA KAGA ABINDA ZAKA CINKA KASAMI KYAUTAR KATI A KARAWAR ARSENAL DA ASTON VILLA

                      MATCH DAY
ARSENAL VS ASTON VILLA
TIME: 8:15PM.


Acigaba da gasar Primier league ta kasar England mako na 8 kungiyar Arsena zata karbi bakwanci Aston Villa a filin wasa na Emirate Stadium. 

Wasan yana da matukar muhimmanci ga dukkan kungiyoyin biyu,  domin kungiyar Arsenal tana bukatar tayi nasara a wannan wasan dan kara kusanto teburin gasar na Primier League. Haka zalika Aston villa suna bukatar suyi nasara a wannan wasan musamman yadda wasanni biyu da suka wuce duk andoke kungiyar ta Aston Villa a gasar na Primier League.

Kushiga cikin nan👇👇

Wannan karawar zai kwashi hankalin yan kallo musamman ganin yadda tsohon mai tsaron ragar Arsenal (Goal keeper) wato Emilino Martinez  zai zo filin wasa Emirate Stadium. Dan wasan zaizo shigo wasanne da burin nunawa Arsenal sunyi kuskure na rashin barinshi a kungiyar yazama mai tsaron ragar kungiyar na farko (First Goal keeper) 
 
MARTINEZ YA AIKAWA DA AUBAMEYANG SAKO AKAN WASAN YAU.

Sabida zakuwa da kosawa da Emiliano Martinez yayi da wannan wasa har yaturawa Aubameyang da sako akan cewa #Allah yasa kasami  bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalty) Ni kuma sai nature bugun naka (Save) wannan shine sakon  da Martinez yaturawa Aubameyang.

Sai dai shima Aubameyang din bayi kasa a guiwa ba wurin maidawa Martinez din Martani inda Aubameyang din yace masa to babu damuwa kashiryawa  daga kwallo ta saman kanka (Chiping).

Kushiga cikin nan 👇👇

Wannan wasa dai zai kayatar matuka dan shima mai tsaron ragar Arsenal na yanzu wato Bernd Leno zaiyi kokari nunawa duniya yana gaba da Emiliano Martinez wadda hakan tasa dole Arsenal ta bashi mai tsaron raga na farko (First Goal keeper).
 
Dan haka muma Arsenal zallah Muka ce wannan Sati zamu bada kyautar kati ga duk wadda yaci harsashenmu.

              HARSASHEN YAU!

Harsashenmu na yau shine munaso kowa yayi hasashe akan wana dan wasa ne zai shawa Arsenal kwallon karshe?

Ma'ana idan kwallaye biyu Arsenal zasu sha to wazaisha ta biyun? Idan kuma kwallaye 3 ne to wazaisha ta ukun?

Wannan shine harsashen wasan yau.

Mutum na farko da harsashensa yafara zuwa dai dai zamu bashi kyautar katin waya.

#Misali mutum 20 suce Aubameyang to zamu duba acikin wadannan mutanen wa yafara Comment da cewa Aubameyang to da mungane wadda shine na farko to zamu bashi kyautar katin waya.

Amma kyautarmu muna badawa ne kawai idan har Arsenal sukayi Nasaara.

Kushiga kugani 👇👇

#Misali Arsenal tayi rashin nasara daci 2-3 to anan matakin babu maganar kyautar kati.

Amma  matukar Arsenal tayi nasara to Insha Allahu zamu bada kyautar kati.

Kuma ko da 1-0 Arsenal din sukayi to nanma zamu bada kyautar kati. Ma'ana harsashenmu na yau yana maganane akan wadda yasha kwallon karshe.
Idan kuma 1-0 akayi to kunga wannan itace kwallon Farko da kuma ta karshe to nan ma zamu bada kyautar.

Dan Allah a Facebook mukeso kowa yayi harsashe adaina yi a Whatsapp.

ARSENAL VS ASTON VILLA
TIME: 8:15PM.


MUNA TAYA HECTOR BELARIN MURNA!

Mai tsaron bayan Arsenal wato Hector Bellarin yasami katin gayyata daga kasarsa ta Sifaniya (Spain) dan wasan wadda yafara wannan kakar wasan da kafar dama yasami wannan gayyatar ne bayan da ya haskaka a wasanni Arsenal inda dan wasan yataimaka aka sha kwallo (Assits) har sau hudu aduk kanin wasan da yabugawa kungiyar ta Arsenal a wannan kakar wasan.

Kushiga nan 👇👇

Kasar Sifaniya (Spain) dai sunkira Hector Bellarin ne dan ya wakilci kasar a wasan da zasuyi  da kasashen da suka hada da...  Ne'dilan (Netherlands),  Siwizilan (Switzerland) da kuma kasar Jamanin (Germany) zasu buga wasannin ne a ranakun 11/11/2020,  14/11/2020, da kuma ranar 17/11/2020. Allah ya tsare rauni Hector Bellarin.

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal cikin harshen hausa.

Naku
Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post