ARTETA YANA SHIRIN YIN GYARA GA YAN WASAN GABAN ARSENAL!!

MIKEL ARTETA YACE ZAIYI DUBA GA YAN WASAN GABAN SHI.


Kocin Arsenal mikel Arteta yace dole zayi gyara ta musamman ga yan wasan gaban shi da yake fara wasa dasu.

Arteta  dai yana fara wasane da yan gaba mutum 3 wato Aubameyang,  Lacazette,  da kuma Willian. To amma wadannan yan wasa da ake fara wasa dasu basu tabuka wani abin azo agani.

Arteta yace tun bayan dawowa daga wasan kasashe da aka buga a watan da yagabata yan gabanmu basu haskakawa hakan yasa dole zamuyi gyara mu duba waye baya kokari?  Dan muga wana gyara zamuyi awurin.

Kushkga cikin nan👇👇
 
Arsenal sunbuga wasanni 4 a gasar Primier League amma kwallo day (1) tak suka iya zurawa a zare.

Arsenal sunbuga wasanni hudu (4)  batare da sun'iya shirya kwallo sun zurata a zare ba. Sunyi wasa da ManCity basu iya saka kwallo acikin raga ba,  Sunyi wasa da Liecester City nan ma haka,  sunyi wasa da Manchester United sai bugun daga kai sai mai tsaron raga (Penalty) aka basu. Sai wasan Aston Villa nan ma sunkasa saka kwallo acikin raga. Rabon kungiyar da ta sha kwallo wadda tashirya a gasar Primier League tun wasan da kungiyar ta doke Shefield United daci 2-1.

Wasa 4 amma kwallo daya tak suka iya jefawa acikin raga,  dayarma daga bugun daga kai sai mai tsaron raga suka sha.

Hakan yasa kocin Arsenal mikel Arteta yace yazama dole yayi gyara ga yan wasan gaban kungiyar,  zai duba cikin mutum 3 da ake fara wasa dasu wanenen baya bawa kungiyar gudunmawa,  waye kuma wadda baya kokari kwata kwata.

Arteta yace zamuyi gyara yadda yakamata akan wannan matsala tamu na rashi zura kwallo acikin zare.

Kudannan nan 👇👇


ANTAMBAYI ARTETA KO HAKAN ZAISA YADINGA FARA WASA DA NIKOLAS PEPE?


Eh! Ina duba yiwuwar fara wasa dashi,  bama shi kadai ba akwai wasu yan wasan da yakamata mufara gwadasu. Zanyi duba ta yadda zanfara wasa da pepe amma dole sai munyi gyara yadda yakamata dan gudun samun wata matsala.

TUNDA NAFARA AIKI A KUNGIYAR BANTABA GANIN YAN WASA NA SUNBUGA WASA MAI MUNI KAMAR NA ASTON VILLA BA.


Kocin Arsenal mikel Areta yace tunda yazo yafara aikin horaswa a kungiyar baitaba ganin kungiyar tashi ta buga wasa mai muni kamar wasan da kungiyar tasha kashi a hannun aston villa ba.


Arteta yace zaiga wana mataki zai dauka,  kafin yaga irin matakin da yan wasansa zasu dauka.  Dole ne muyi gyara yadda yakamata.

Kushiga kugani👇👇

SAKON EMILIANO MARTINEZ BAYAN DA ASTON VILLA SUKA DOKE ARSENAL!!

Tsohon mai tsaron ragar Arsenal wato Emiliano Martinez yace  na kwashe shekaru goma da kungiyar Arsenal watanni biyu da suka wuce na lashe kofuna biyu da kungiyar,  Amma a wasan da na fuskanci kungiyar nashigo wasanne da fatan yin nasara akansu,  nakuma yi nasarar sabida ni mai nasara ne,  kuma ni dan Kasar Argentinane. Ina girmama Arsenal.

MEZAKACE AKAN BARINKA ARSENAL??

Nakira Arteta nace masa ni inada bukatar duk sati na buga wasa,  Amma sai yacemin hakan bazai samuba. Ko kafin wasan karshe da mukayi da Liverpool na kofin Community Shield Arteta baisan dawa zaifara wasa acikinmu ba.

Kafin wasan Fulham sai natura masa sakon waya aka yataimaka min ni inason zantafi Aston Villa.


PEPE YACE YANA BUKATAR BUGA WASANNI SOSAI!!

Nicolas Pepe yace bayajin dadin rashin buga wasa da bayayi a kungiyar Arsenal.

Kudanna nan 

Dan wasan dan kasar Ivory Coast yace dole dan wasa yaji babu dadi aduk lokaci da ya kasance baya samun buga wasa yadda yakamata. Amma zanyi iya kokarina dan ganin nasami wasa yadda yakamata a kungiyar.

 KO ZAKA'IYA ZUWA KUNGIYAR TOTTEHAM??

Antambayi tsohon dan wasan Arsenal wato jack Wilshere shin ko zai'iya zuwa kungiyar Totteham?

Sai dan wasan yace a gaskiya inason Jose Mourinho sabida yakasance mai horaswa da yake da basira. To amma maganar gaskiya bazan taba zuwa Totteham ba sabida kasancewata dan Arsenal.

Dan wasan dai ayanzu haka baida kungiya tun bayan da Westham United suka janye kwantaraginsa a watan da ta gabata.

TONNY ADAMS YANA KIRA GA ARTETA AKAN YADAWO DA OZIL CIKIN KUNGIYAR ARSENAL!!

Tsohon dan wasan Arsenal wato Tonny Adams yace yana kira ga kocin Arsenal Wato Mikel Arteta da yadawo da Mesut Ozil cikin tawagar yan wasan Arsenal.

Kushiga👇👇👇
Adams yace ni awurina duk duniyar kwallo ayanzu babu wani dan wasa da ya'iya bada kwallo aci ko ya kirkiro yadda za'aci kwallo kamar Mesut Ozil.

Zanso naga Ozil kusa da Aubameyang yana bashi kwallo yana jefata cikin zare kullum,  kamar yadda Dennis Bergkamp yadinga bawa Henry. Ina ganin akwai abubuwa da yawa wadda sukayi kamanni tsakaninsu (Aubameyang &Ozil,  Bergkamp&Henry).


Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal cikin harshen hausa.

Naku
Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post